An kashe Basarake, matarsa da mutum 3 a Benuwe

Harin ya faru ne a daren ranar Alhamis, inda maharan suka isa kan babura biyu, suka far wa gidan Basaraken tare da buɗe masa wuta shi da iyalansa.

An kashe Basarake, matarsa da mutum 3 a Benuwe

Rahonni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyar, ciki har da wani basaraken gargajiya, matarsa da ɗansa da wasu mazauna garin su biyu a yankin Olegabulu da ke ƙaramar hukumar Agatu a Jihar Benuwe.

Mazauna yankin sun bayyana wa wakilinmu cewa, harin ya faru ne a daren ranar Alhamis, inda maharan suka isa kan babura biyu, suka far wa gidan Basaraken tare da buɗe masa wuta shi da iyalansa.

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan su huɗu ne suka gudanar da wannan aika-aika.

A cewarsa, sun shigo garin ne ba tare da zargin kowa ba, kai-tsaye suka nufi fadar inda suka harbe Basaraken, matarsa da ɗansa har lahira.

Ya ƙara da cewa, ’yan bindigar sun koma wani gida na kusa, inda suka kashe wasu mazauna garin biyu kafin su tsere.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa, maharan sun haɗu da mutanen gari tun da fari, har ma suna gaisa da mutanen cikin yaren yankin.

“Maharan ba Fulani ba ne. Lokacin da suka zo, sun yi mu’amala da mutane cikin yarenmu, don haka babu wanda ya yi zargin cewa maƙiya ne. Amma da zarar da suka shiga gidan Sarkin, sai suka buɗe wuta, mutane suka fara gudu don tsira da rayukansu.

Sun kwashe kusan mintuna 20 suna wannan aika-aika. Bayan sun kai hari gidan sarkin, sun koma wani gida na kusa suka kashe wasu mutane biyu. An samu wani mutum ɗaya da ya samu rauni kafin su gudu,” in ji wani shaida.

Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Melɓin Ejeh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutum biyar ne aka kashe yayin da mutum ɗaya ya ji rauni.

Ejeh ya ƙara da cewa, jami’an tsaro ciki har da ’yan sanda sun ziyarci wurin da abin ya faru.