Majalisar Dokokin Jigawa ta bada umarnin bincikar Gwamnatin Badaru
Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar, wanda ya gudanar da cikakken bincike kan bayanan kuɗi na ma’aikatu
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin kuɗaɗe na hukumomin gwamnati, inda ta bayar da umarnin a ƙwato kuɗaɗen da aka gano ta wata hanya daban.
Za a ƙwato kuɗaɗen aka gano akwai matsala a kansu a wani babban binciken kuɗi da ya shafi lokacin mulkin tsohon Gwamna, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
- Mutane 12 daga cikin 416 da Boko Haram ta sace sun tsere — BOSYA
- Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika
Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar, wanda ya gudanar da cikakken bincike kan bayanan kuɗi na ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati, da kuma ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Da yake gabatar da rahoton a zaman majalisa, shugaban kwamitin, Hon. Isyaku Abubakar, ya bayyana cewa binciken ya samo asali ne daga rahotannin ofisoshin Babban Mai Binciken Kudi na Jiha da na ƙananan Hukumomi, tare da gudanar da sauraron ra’ayoyin jama’a da halartar manyan jami’an gwamnati.
Ya ce, an gayyaci kwamishinoni, sakatarori na dindindin, daraktocin kuɗi da shugabannin ƙananan hukumomi domin yin ƙarin bayani kan wasu mu’amalolin kuɗi, inda kwamitin ya tabbatar da bin ƙa’idoji a duk tsawon aikin.
Rahoton ya bayyana wasu matsaloli da suka haɗa da rashin cikakkun takardu, saɓani a bayanan kashe kuɗi, da kuma rauni kan tsarin sa’ido a matakin jiha da ƙananan hukumomi.