Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu

Yawancin jami’an tsaron da aka kashe, ’yan bindiga ne suka halaka su yayin da suke ƙoƙarin kare al’umma a lokacin hari, yayin da wasu kuma aka kashe su a shingayen binciken tsaro da sansanoninsu

Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu

Aƙalla jami’an tsaro 53 aka kashe a sassa daban-daban na Nijeriya cikin makonni biyu da suka wuce, bisa ga ƙididdigar da muka tattaro daga rahotannin kafofin yaɗa labarai.

Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da sojoji da ’yan sanda da jami’an Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula (NSCDC), jami’an shige da fice da na kwastam, da ma jami’an sa-kai da ke taimaka wa jami’an tsaro, ciki har da ’yan sa-kai na JTF da na ƙungiyoyin tsaro na al’umma da gwamnatocin jihohi suka kafa.

Yawancin waɗanda aka kashe, ’yan bindiga ne suka halaka su yayin da suke ƙoƙarin kare al’umma a lokacin hari, yayin da wasu kuma aka kashe su ne a wuraren binciken tsaro da sansanoninsu.

Wannan adadi ya taƙaita ne kan alkulman da muka tattara daga rahotannin kafofin yaɗa labarai, bai haɗa da wasu hare-haren da ba a bayyana su ba ba.

Wani bincike da muka gudanar a watan Disambar bara ya nuna cewa, daga watan Janairu 2023 zuwa Oktoba 2024, aƙalla jami’an ’yan sanda 229 aka kashe a faɗin ƙasar nan.

Binciken ya bayyana cewa ’yan bindiga, ’yan ƙungiyar IPOB da ’yan Boko Haram da ’yan fashi da makami da kuma ’yan ƙungiyoyin asiri ne suka kashe jami’an tsaron.

Sabbin hare-haren sun faru ne a jihohin Benue da Kogi, inda aka kashe ’yan sanda bakwai da wasu jami’an tsaro a lokuta daban-daban a ranar Juma’a da kuma jiya Lahadi.

Baya ga waɗanda aka kashe, an kuma sace wasu jami’an tsaro a harin da aka kai a Binuwai.

A ’yan kwanakin nan, Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar da mutane tara a gaban kotu bisa zargin hannu a kisan gilla da aka yi a jihohin Binuwai da Filato.

An kai su gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda kuma aka tuhumi wani da ake zargi da fataucin makamai bisa mallakar bindigogi ƙirar M16 guda bakwai ba bisa ƙa’ida ba.

Cikin waɗanda aka gurfanar har da Haruna Adamu da Muhammad Abdullahi, ’yan asalin Karamar Hukumar Awe a Jihar Nasarawa, da ake tuhuma da laifuka huɗu kan kashe-kashe a Abinsi da Yelewata a Ƙaramar Hukumar Guma ta Jihar Binuwai a ranar 13 ga watan Yuni.

Haka kuma an gurfanar da Terkende Ashuwa da Amos Alede, dukkansu daga Guma, kan zargin kai farmaki don ramuwar gayya da kuma lalata dukiya, wanda ya haddasa salwantar shanu 12 a garin Ukpam.

Jerin Kashe-kashenjami’an tsaro a Satumba

– 4 Satumba: An kashe ɗan sanda da ɗan sa-kai na JTF bayan ’yan bindiga sun yi musu kwanton bauna a yankin Mada na Karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara. Haka kuma a ranar, wasu da ake zargi ’yan tawayen ne suka kashe ’yan sanda biyu a harin da suka kai a iyakar Obehie da ke tsakanin jihohin Ribas da Abiya.

– 5 Satumba: ’Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC guda takwas da ke aiki a masana’antar siminti ta BUA da ke Okpella, Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas, Jihar Edo.

– 6 Satumba: An kashe jami’an shige da fice biyu a harin da ake zargin ’yan Boko Haram suka kai a Ƙaramar Hukumar Monguno, Jihar Borno. A rana ɗaya kuma, ’yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro (Community Watch Corps) na Jihar Katsina kwanton ɓauna a Ɗandume, inda suka kashe mutane takwas tare da ƙona motocin sintiri guda biyu.

– 8 Satumba: An kashe jami’in NSCDC guda ɗaya a Abuja bayan abokin aikinsa ya harbe shi da kuskure a unguwar Life Camp.

9 Satumba: A Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma, Jihar Kogi, ’yan bindiga sun kashe ’yan sanda uku da sa-kai biyu a kwanton ɓauna a wuraren binciken tsaro.

– 10 Satumba: Sojoji biyar sun mutu a kwanton ɓauna yayin sintiri a Gusau, Jihar Zamfara.

– 15 Satumba: ’Yan bindiga sun yi wa jami’an NSCDC kwanton ɓauna a kan hanyar Yantumaki–Danmusa, Dafa, Jihar Katsina, inda suka kashe jami’i guda ɗaya.

– 17 Satumba: An kashe jami’in Kwastam guda ɗaya a wurin bincike a Karamar Hukumar Dandi, Jihar Kebbi. A ranar kuma, an kashe wani ɗan sa-kai a artabu da masu garkuwa da mutane a yankin Kpaduma, Abuja.

– 18 Satumba: A Jihar Kwara, an kashe kwamandan ’yan sa-kai, yayin da aka kashe ɗan sanda a Jihar Enugu. Haka kuma, ’yan ta’adda sun kai hari sansanonin soja a Banki, Ƙaramar Hukumar Bama, Jihar Borno, inda aka kashe sojoji biyu.

Daga:

Sagir Kano Saleh, Abdullateef Salau, Idowu Isamotu (Abuja), Hope Abah (Makurdi), Tijjani Labaran (Lokoja) & Abubakar Akote (Minna)