An kashe mutum 1 a rikicin magoya bayan masu neman takarar Gwamnan Nasarawa a APC

Magoya bayan Sanata Wadada da na tsohon Shugaban ’Yan Sanda Mohammed Adamu sun ba kamata iska, har da asarar rai

An kashe mutum 1 a rikicin magoya bayan masu neman takarar Gwamnan Nasarawa a APC

Wasu matasa a yayin rikicin zaben shugaban kasar Kamaru na 2025, wanda Shugaba Paul Biya mai shekara 92 ya lashe da kaso 53 domin fara wa’adinsa na takwas na tsawon shekara bakwai

Mutum ɗaya ya rasu sakamakon rikici tsakanin magoya bayan wasu masu neman takarar Gwamna Jihar Nasarawa a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC.

Lamarin ya faru ne a unguwar Tudun Gwandara da ke garin Lafia, babban birnin Jihar.

Mamacin mai suna Abbas Rabiu ya samu mummunan rauni a kai yayin rikicin, daga bisani ya rasu a Asibitin Koyarwa na Gwagwalada inda aka kai shi domin jinya, a cewar Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Nasarawa kan harkokin siyasa, Adamu Musa Alƙali.

Alkali, wanda mazaunin yankin Tudun Gwandara ne kuma jigo a yankin, ya ce an shirya taron ne domin nuna goyon baya ga amincewa da Sanata Wadada a matsayin ɗan takarar da Gwamna Abdullahi Sule take goyon baya.

Ya shaida wa manema labarai cewa an bi dukkan matakan da suka dace kafin gudanar da taron, ciki har da sanar da rundunar ’yan sanda ta B Division da ke Lafia, da sauran hukumomin tsaro.

A cewarsa, rikicin ya fara ne lokacin da wani mai suna Ɗann’iya Sambo ya isa wurin taron da fastoci da alluna da kuma kayan sauti masu nuna goyon baya ga mai neman takarar gwamna kuma tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu Abubakar, sannan ya fara tara magoya baya a wurin.

“Da ya tara mutane, sai suka zo suna ƙoƙarin kutsawa cikin tsakiyar taron. Suka fara dukan mutane da lalata kayayyaki tare da kwashe wasu abubuwa,” in ji Alkali.

“Wasu mutane suka yi ƙoƙarin kare kansu, a nan ne aka bugi wani mutum a kai da adda, wanda hakan ya janyo mutuwarsa.”

Ya ce da farko an kai Rabiu Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya kafin daga bisani a mayar da shi Asibitin Koyarwa na Gwagwalada domin yi masa tiyata.

Alƙali ya ce an sanar da iyalan mamacin da misalin karfe 2 na daren ranar Juma’a cewa ya rasu.

Sai dai wani magoyin bayan tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu Abubakar, mai suna Jibrin Ali Baggio, ya bayar da wani bayani daban kan yadda lamarin ya faru.

Baggio ya ce rikicin ya faru ne a ƙofar gidan Dan’iya Sambo, wanda ya shirya wani taron siyasa da ƙarfe 7 na safe a matsayin wani ɓangare na gangamin wayar da kan al’umma a unguwa.

Ya ce Ɗan’iya da sauran magoya bayansa sun fara taron ne kafin wata kungiyar mutane ta iso da misalin karfe 9 na safe domin gudanar da nasu taron a wuri guda.

A cewarsa, Dan’iya ya nuna rashin amincewa da hakan, yana mai cewa ana gudanar da taron ne a unguwarsa kuma a ƙofar gidansa.

“Mai unguwa ya dakatar da dayan ɓangaren saboda ba mutanen yankin ba ne kuma suna gudanar da taro a ƙofar gidan wani,” in ji Baggio.

“Lokacin da suka ƙi amincewa, sai faɗa ya barke.”

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mutanensu sun samu raunuka a rikicin, ciki har da wani da aka ji wa ciwo a kai da wani da aka ji wa rauni a kunne, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.

Bayan rikicin, Baggio ya ce an shawarci Ɗan’iya da ya kai rahoto ofishin ’yan sanda.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya ce rundunar ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba har zuwa lokacin da aka tuntuɓe shi.

Sai dai Kakakin Hukumar NSCDC ta Jihar Nasarawa, Jerry Victor, ya ce jami’ansu sun isa wurin rikicin tare da taimakawa wajen dawo da zaman lafiya.

Rahotanni sun ce tarukan na daga cikin gangamin tuntuɓar al’umma da magoya bayan masu neman takarar gwamna a APC ke gudanarwa gabanin zaɓen fid-da-gwani  na jam’iyyar.