Mutum 16 sun mutu a hatsarin mota a Kogi

Shaidu sun bayyana cewa motar ta faɗa a cikin wani babban rami ne, bayan kauce daga kan hanya a yayin da take ƙoƙarin haye wata gada

Mutum 16 sun mutu a hatsarin mota a Kogi

Aƙalla mutum 16 ne suka mutu yayin da wasu shida suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a ƙauyen Aku, a kan hanyar Lokoja zuwa Okene da misalin karfe 9:20 na safiyar ranar Juma’a.

Shaidu sun bayyana cewa motar ta faɗa a cikin wani babban rami ne, bayan kauce daga kan hanya a yayin da take ƙoƙarin haye wata gada.

Rahotanni sun ce mutane 22 ne a cikin motar ƙirar Toyota Hiace, a yayin da take kan hanyarta ta zuwa Legas da su, daga Jos, babban birnin Jihar Filato.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Kogi, Lawal Fagge, ya bayyana cewa ya yi sanadin mutuwar mutum 16 ciki har da mace daya tilo da ke cikin motar.

Ya bayyana cewa gajiya da kuma gudu fiye da ƙima da direban motar ya yi ne suka haddasa hatsarin.

Fagge ya ce hukumar ta tura tawagar ceto daga sashen Zariagi zuwa wurin domin kwashe waɗanda abin ya shafa tare da cire tarkacen motar bayan samun rahoton faruwar lamarin.

“Ana kan hanyar zuwa Legas daga Jos ne wata mota mai kujeru 18 ɗauke da fasinjoji 22 a cikinta, ta yi hatsari. Mutum 16 sun mutu nan take, mutum biyar sun samu munanan raunuka, yayin da mutum ɗaya bai samu ko ƙwarzane ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira ya shaida musu cewa fasinjojin sun buƙaci direban ya tsaya ya huta bayan sun lura yana cikin gajiya, amma ya ƙi saurarar su har sai da ya yi hatsarin a kusa da gadar da ke kan hanyar.

Fagge ya ce hukumar ta tura tawagar ceto daga sashen Zariagi zuwa wurin domin kwashe waɗanda abin ya shafa tare da cire tarkacen motar bayan samun rahoton faruwar lamarin.

Ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti a Lakwaja domin samun kulawa, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin ajiye gawa na Ankuri da ke Lakwaja.

Shugaban FRSC na jihar ya buƙaci masu amfani da hanya da su kasance masu lura tare da bin dokokin tuƙi domin kauce wa haɗurran da za a iya kauce musu a manyan hanyoyi.

An gano baƙin haure 30 a ɓoye cikin tankar mai a Turkiyya

An tsare ɗan gwagwarmaya kan sukar gwamnatin sojin Nijar

Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida

Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida