An lakada wa Fasto da ɗan cocinsa duka kan zargin satar mazakuta

Daga bisani ’yan sanda sun yi nasarar cetar mutanen

An lakada wa Fasto da ɗan cocinsa duka kan zargin satar mazakuta

Dukan ‘yar aiki

Wani Fasto a cocin Deeper Life da ke Kanshio a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai, ya sha duka shi da wani dan majami’arsa ranar Asabar bisa zarginsu da satar mazakuta.

Bayanai sun nuna matasa ne suka fara dukan dan cocin mai suna Jude Tyokula, bayan da wani mutum da ba a kai ga tantance shi ba ya yi kururuwar an sace masa mazakutar tasa.

Daga nan ne dai wanda ake zargin ya ambaci Faston nasa mau suna Terna, a matsayin wanda ya aike shi.

Sai dai bayan sun sha dukan, ’yan sanda sun sami nasarar ceto su daga hannun matasan, inda suka wuce da su caji ofis dinsu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Catherine Anene, ce ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce, “Na sami wadannan mutanen a ofishinmu na B Division ranar Lahadi, da suka bayyana min abin da ya faru, na tausaya musu.

“Wasu ne kawai suka yi zargi, sai wadannan fustatattun matasan suka hau duka wadannan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da duka. Wannan abin alla-wadai ne kuma rashin imani ne.

“Bayan sun rufe shi da duka, sai ya ce musu shi Faston shi ne ma ya aike shi, bisa tunanin za su yi masa afuwa, amma sai suka hada su su biyun suka zane.

“Kuma duk wannan fa karya ne, tun lokacin da aka fara wannan kururuwar, babu wanda aka taba tabbatarwa an sace masa,” in ji Catherine.

Kakakin ta ce kodayake ba su kai ga kama kowa daga cikin matasan da suka yi dukan ba, amma suna nan sun baza komarsu.