An sako ragowar daliban FGC Birnin Yauri

Baya shekara biyu, an gama sako daukacin dalibai 96 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su daga FGC Birnin Yauri

An sako ragowar daliban FGC Birnin Yauri

FGC Yauri

’Yan bindiga sun sako dalibai mata uku da suka rage a hannunsu daga cikin yara 96 da suka sace a Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke birnin Tauri a Jihar Kebbi.

A ranar Litinin ’yan matan suka dawo hannun gwamantin jihar bayan ’yan bindigar sun sako su a ranar Lahadi.

Kakakin kungiyar daliban da aka yi garkuwa da su a FGC Birnin Yauri, Salim Kaoje, ya tabbatar wa Aminiya cewa, “An sako dalibai uku da suka rage da almurun ranar Lahadi, yanzu haka suna hannun gwamnatin jiha.”

Ya ce wadanda aka sako din su ne Aliya Abubakar da Elizabeth Ogechi Nwafor da kuma Esther Sunday.

Sai dai bai bayyana ko an biya kudin fansa kafin a sako su ba.

Ko da yake a a watan Afrilu da ’yan ta’adda suka sako karin mutum hudu daga cikin daliban, Kaoje ya bayyana cewa mahaifiyar Dogo Gide — dan ta’addan da ya yi garkuwa da yaran ta sanya baki ya sako su — amma duk da haka sai da ya karbi kudin fansa.

Kaoje ya bayyana cewa, iyayen daliban ne suka sayar da kadarorinsu suka tara kudin da kuma taimakon da suka samu daga jama’a suka bayar a matsayin kudin fansa kafin a sako yaran.

Shekara biyu da suka wuce, a ranar 17 ga watan Yuni, 2021  ne Dogo Gode da yaransa suka kai hari FGC Birnin Yauri suka sace dalibai 96.

Daga baya suka sako wasu daga cikin daliban, a lokuta daban-daban, kafin a ranar Lahadi a sako mutum uku da suka rage.

Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu