An shiga tsaka mai wuya bayan ’yan tawaye sun kashe Ministan Tsaro a Mali

Har yanzu dai ba a ji ɗuriyar Janar Assimi Goita ba, wanda aka daina gani tun da aka fara hare-haren a ranar Asabar.

An shiga tsaka mai wuya bayan ’yan tawaye sun kashe Ministan Tsaro a Mali

Jagororin mulkin sojin Mali sun shiga tsaka mai wuya, biyo bayan hare-haren haɗin gwiwa da ’yan ta’adda da ’yan tawayen Abzinawa suka kai cibiyar gwamnati a ƙarshen mako.

Bayanai sun ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar Ministan Tsaron ƙasar Sadio Camara, sannan rahotonni na nuna cewa wani babban birnin arewacin ƙasar ya faɗa hannun maharan.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa Janar Sadio Camara ya mutu ne tare da matarsa ta biyu da jikokinsa biyu, bayan wani harin bam da aka dasa a cikin wata mota a kusa da gidansa da ke birnin Bamako.

Majiyoyi daga iyalansa da hukumomi sun ce harin, wanda aka kai ranar Asabar, ya hallaka shi tare da wasu daga cikin ’yan uwansa, inda ake zargin mayaƙan da ke da alaƙa da Al-Qaeda da hannu a kai.

Harin ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin ’yan tawaye da masu iƙirarin jihadi suka ƙaddamar da hare-hare a wurare da dama na ƙasar, ciki har da Kati—wata muhimmiyar cibiyar sojojin gwamnatin mulkin soja.

A jiya Lahadi dai an ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da ’yan tawayen Abzinawa ta FLA da kuma wasu ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ke mara musu baya.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai hare-hare a garuruwan Kidal, Gao da Sévaré, inda suka yi amfani da manyan makamai wajen kai farmaki kan sansanonin sojoji.

Janar Camara na daga cikin manyan hafsoshin sojin da suka jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a 2020, kuma ana kallonsa a matsayin muhimmin jigo a tafiyar gwamnatin mulkin soja ta ƙasar.

Mutuwarsa na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin tsaro ke ƙara tsananta a ƙasar, lamarin da ke ƙara jefa damuwa kan makomar zaman lafiya a Mali.

Har yanzu dai ba a ji ɗuriyar shugaban mulkin sojin Mali, Janar Assimi Goita ba, wanda aka daina gani tun da aka fara hare-haren a asubahin Asabar da ta gabata.

Masana sun ce waɗannan hare-haren su ne ƙalubale mafi girma da jagororin sojin Mali suka fuskanta tun bayan farmakin watan Maris na shekarar 2012.