Cutar sankarau ta kashe mutum sama da 20 a Sakkwato

Wasu mazauna da suka bukaci a sakaya sunayensu sun ce akalla mutane 40 sun mutu a kauyen da makwabtansu.

Cutar sankarau ta kashe mutum sama da 20 a Sakkwato

Ana fargabar barkewar cutar sankarau ta yi ajalin gomman mutane a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.

Mazauna yankin sun bayyana damuwa a yayin da majiyoyi a cibiyar kula da lafiya da ke kauyen sun bayyana cewa lamarin na kara tsanani a baya-bayan nan, inda a kullun ake asarar rayuka biyu zuwa uku, yawancinsu masu shekaru biyu zuwa 20 da haihuwa.

Majiyar ta bayyana yadda ake samun karuwar majinyata, a yayin da jama’ar yankin ke bayyana damuwa. “Kullum mutane suna yin tururuwar zuwa ganin likita. Abin ya fi karfinmu kuma ba mu san ainihin abin da ke kashe mutane kusan kullum ba,” a cewar majiyar.

Majiyoyi sun bayyana cewa wasu daga cikin majinyatan sun rsu ne kafin a gano cutar, inda daga bisani aka shawarce su do su guji kwana cikin daki da ke rufe saboda yanayin tsananin zafi da ake ciki.

“Yawancin mace-mace sun auku ne kafin a ganon cewa cutar sankarau ce. Dsaga bisani aka shawarci mutane guji kwana da cikin daki a rufe saboda tsananin zafi, amma duk da haka an ci gaba da samu asarar rayuka,” a cewar majiyar.

Mazauna yankin sun bayyana cewa alamomin cutar sun hada da ciwon wuya, amai, gudawa, zazzabi mai tsanani, da galabaita kuma kumbar baki.

“Wani lokaci yaro zai fara korafin ciwon wuya kafin ya nuna alamun gabaita,” a cewar majiyar.

Duk da daukin da suka samu, al’ummar yankin sun bayyana damuwa cewa cutar ba ta lafa ba, lamarin da ya haifar da fargabar cutar sankarau ce.

“An cewa mana cutar sankarau ce, amma abin bai tsiya. Shi ya sa ake zargin ko wata cutar ce ta daban,” a cewar wani mazaunin yankin.

Wasu majiyoyi na cewa duk da yake an kai rahoton lamarin, amma daukin da suka samu bai kai ya kawo ba, sai da aka turo jami’i daga Ofishin Sanya Ido Kan Bullar Cututtuka zuwa yankin.

“Sun turo jami’in da ke ziyartarmu kullum. Ya dauki samfuri kuma yana turo rahoto a kowace rana. Amma zuwa yanzu dai ba mu san inda aka kwana ba,” in ji majiyar.

Wasu mazauna da suka bukaci a sakaya sunayensu sun ce akalla mutane 40 sun mutu a kauyen da makwabtansu.

Amma wata majiya a cibiyar lafiyar ta bayyana cewa mutum uku ne ake da bayanin rasuwarsu a cibiyar lafiyar, inda ta bayyana cewa yawancin mutanen sun rasu ne a gida.

“Mutum uku ne suka rasu a asibiti, amma yawancinsu a gida suka rasu. Yawanci ba a kawo majinyata asibiti da wuri; maganin gargajiya suke yi, sai idan abin ya yi muni suke zuwa,” a cewar majiyar.

Ta bayyana cewa yawancin majinyatan sukan rasu ne cikin awa 24 bayan alamun cutar ta bayyana a jikinsu.

“Yawancinsu suna mutuwa ne cikin 24 bayan nuna alamar cutar,” a cewarta.

Wani mazauni yankin, Surajo Saidu, ya ce har yanzu ba su da tabbaci game da ainihin yanayin cutar, wadda ta kai mutane da dama asibiti.

“Kimanin mutum 20 sun rasu bayan barkewar cutar. Muna rokon hukumomin lafiya da su gudanar da cikakken bincike domin daukar matakan da suka dace.”