An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa
Wasu zauna gari banza sun burma wa wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) wuka har lahira a Kasuwar Shuwarin da ke ci Karamar Hukumar Kyawa a Jihar Jigawa.
wuka
Wasu zauna gari banza sun burma wa wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) wuka har lahira a Kasuwar Shuwarin da ke ci Karamar Hukumar Kyawa a Jihar Jigawa.
Kakakin Hukumar NSCDC reshen Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya bayyana cewa an kai wa jami’in hari ne a lokacin da yake bakin aiki a ranar Linitin a lsashin sayar da shanu na kasuwar (Kara), inda ’yan iskan suka kai wa jami’in hari.
Ya ce “Maharan da ake zargin suna xauke da wuqaqe ne suka farma jami’in, suka yi masa mummunar varna, inda maharan suka far wa jami’in da wukake, kuma abin takaici, ya rasa ransa nan take.
Kakakin ya bayyana cewa, “Wanda abin ya shafa mai suna Sufeto Bashir Adamu Jibril, ma’aikaci ne a sashin bincike na hukumar NSCDC ta jihar Jigawa.
- Majalisa ta amince da sabuwar Dokar Masarautun Katsina
- Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya
An garzaya da shi zuwa babban asibitin Dutse inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa, kuma an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da wasu da dama kuma suka gudu.
Rundunar ta yi Allah wadai da lamarin tare da tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci. “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kotu”, in ji Tijjani.