Majalisa ta amince da sabuwar Dokar Masarautun Katsina
Dokar ta ba wa gwamna kadai ikon daga darajar sarki da kuma nada karin mutum a cikin masu zaben sarki
Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina ta amince da sabuwar Dokar Masarautu ta jihar, bayan ta yi wa daftarin dokar karatu na daya har zuwa na uku.
A sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima, wadda take jiran sa hannun Gwamna Umaru Dikko Radda, gwamnan jihar ne kadai ke da ikon daga darajar sarki.
Kazalika ta ba wa gwamnan jihar kadai ikon zabar wani mutum ya kara a cikin masu zabar sarki, sa’annan ta kara yawan da masu zaben sarki daga mutane hudu zuwa biyar.
Kauran Katsina, Galadiman Katsina, ’Yandakan Katsina da Durbi su ne mutum hudu da aka sani a mastayin masu zabar sarki, amma yanzu dokar ta da Marusan Katsina Hakimin Shargalle, sarautar da aka ba wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika.
- Gobara ta cinye gidan hakimi a Bauchi
- Nafisa ta cancaci kyautar Dala 100,000 da gida da OON —Pantami
- Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya
A makon da ya gabata ne masarautar ta ba wa Hadi Siriki wannan sarauta wadda aka dauke ta daga Dutsi, yayin da ita Dutsin kuma aka mayar da Baburtau a matsayin mukamin Hakimin.
Gabanin wannan sabuwar doka a satin da ya gabata ne Masarautar Katsina ta fitar da sunayen wasu hakiman da aka kirkiro a masarautar.
Bayan waccan sanarwa, sai kuma ga kwafin ita wannan doka wadda majalisar ta yi wa karatu na yawo a kafofin sada zumunta.
Kazalika, akwai ’yan Majalisar Masarautun na Katsina da Daura wadanda aka yi wasu canje-canje.
A yanzu ’yan majalisar sun qunshi wakilai biyu da malamai, biyu daga attajiran jihar, wakili daga sashen kungiyoyin matasa. Sauran su ne, wakilin Kwamishinan Kananan Hukumomi, wakili daga Ma’aikatar Masarautu da masu zaben sarki.
Hatta da Sakataren Majalisa za a turo shi ne daga gwamnati maimakon a da sarki ne ke zabar shi.