An yi addu’o’i don tunawa da Sarkin Kano Usman II bayan shekaru 100 da rasuwarsa
Sarakuna da manyan malamai na daga cikin waɗanda suka halarci taron addu’ar.
An gudanar da taron addu’o’i na musamman a Babban Masallacin Juma’a na birnin Kano, domin tunawa da cika shekaru 100 da rasuwar Sarkin Kano na 52 kuma Sarki na 9 a jerin Sarakunan Fulani, marigayi Alhaji Usman Abdullahi II.
Taron, ya haɗa da addu’o’i da kuma waiwaye kan rayuwa da tarihin marigayin, wanda ya yi mulki daga shekarar 1919 zuwa 1926.
- Gobara ta lalata buhun albasa sama da 5,800 a Sakkwato
- Dubun ɗan banga mai yi wa Boko Haram safarar makamai ta cika a Borno
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ne, ya jagoranci addu’o’in tare da jaddada muhimmancin tunawa da shugabanni na gari da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimta wa al’umma.
Taron, ya samu halartar manyan sarakuna, malamai da shugabannin al’umma daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.
Daga cikin waɗanda suka halarta akwai Sarkin Ringim, Sayyadi Abubakar Mahmud, wanda Chiroman Ringim ya wakilta, da Sarkin Jama’are, Nuhu Ahmad Wabi, wanda jika ne ta ɓangaren uwa ga marigayin.
Haka kuma, Sarkin Machina, Bashir Bukar, da sauran hakimai da masu riƙe da sarautun gargajiya daga Kano, Ringim da Jama’are sun halarta.
Fitattun malaman addini ciki har da Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zahradeen, da Shugaban Majalisar Malamai ta Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, sun jagoranci addu’o’in neman Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya jiƙansa da rahama.
A jawabinsa, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa taron wani muhimmin darasi ne ga al’umma, inda ya buƙaci mutane su dage wajen aikata alheri tun suna raye.
Ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce mafi alherinku shi ne wanda ya daɗe a rayuwa yana aikata ayyukan alheri, mafi muni kuwa shi ne wanda ya daɗe yana rayuwa amma yana aikata munanan ayyuka.
“Wannan taro yana tunatar da mu cewa wata rana duk za mu bar duniya, kuma muna fatan waɗanda muka bari za su riƙa tunawa da mu tare da yi mana addu’a.”
Sarkin ya kuma bayyana cewa Sarkin Ringim shi ne mafi tsufa cikin jikokin marigayi Usman Abdullahi II da ke raye a yau.
Tarihi ya nuna cewa marigayi Sarkin Usman Abdullahi II, ya hau karagar mulki a shekarar 1919 yana da shekaru 76 a duniya, bayan rasuwar Sarki Abbas, wanda shi ne Sarkin Kano na farko da Turawan mulkin mallaka suka naɗa.
Duk da tsufa da rashin lafiya, mulkinsa ya samu manyan nasarori.
Ɗaya daga cikin fitattun abubuwan tarihi a zamaninsa shi ne saukar jirgin sama na farko a Kano a shekarar 1925, wanda kuma shi ne karo na farko a Najeriya, a lokacin ziyarar ɗan Sarkin Ingila, Prince Edward.
Haka kuma, an fara manyan ayyukan more rayuwa a zamaninsa, ciki har da aikin ruwan Chalawa, gidan yari na Goron Dutse, samar da wutar lantarki, asibitoci da gine-ginen ofisoshi.
Ko da yake mulkinsa ya fuskanci ƙalubale sakamakon tsufa, rashin lafiya da kuma tasirin Turawan mulkin mallaka, amma ya kafa tubalin ci gaban Kano.
Bayan shekaru 100 da rasuwarsa, tarihinsa na ci gaba da zama abin koyi ta fuskar shugabanci na gari, gaskiya da kishin al’umma.
Ga hotunan yadda taron ya gudana: