Ana fargabar ruwa da iska sun kashe mutum 2,000 a Libya
Gwamnatin Gabashin Libya, ta yi ikirarin cewa sama da mutum 2,000 sun rasu, wasu dubban kuma sun bace
Ana fargabar mutum kimanin 2,000 sun mutu a kasar Libya sakamakon ruwa da mahaukaciyar idakr Daniel da ta kaɗo daga Tekun Mediterranean.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Ake Yawan Samun Hatsarin Jirgin Ruwa A Neja
- Girgizar kasa: Ya rage na Morocco ta nemi taimakonmu —Faransa
Duk da cewa alkaluman da kafofin yada labarai da ke Gabashin Libya suke bayarwa ke nan, amma wasu bayanan sun nuna girman barnar bai kai haka ba.
Da farko dai Mohamed Massoud, mai magana da yawun gwambatin Hamad da ke Benghazi, ya ce “aƙalla mutane 150 ne suka rasu sa sakamakon ruwa da mahaukaciyar guguwar Daniel a yankin Derna, da ke Lardin Jabal al-Akhdar.
“Iftila’in ya haddasa mummunar asara ga dukiyoyin al’umma da kayan gwamnati,” kamar yadda ya bayyana wa AFP.
Ana fargabar akwai daruruwan mutane da suka makale a wurare masu wuyan zuwa a sakamakon ambaliyar, a yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Hukumomin yankin Gabashin Libya sun ce sun daina jin ɗuriyar wasu sojojinsu tara a yayin da suke tsaka da gudanar da aikin ceton.
Hamad da kansa yake jagoranta aikin ceto inda ya jagoranci sauran ministoci zuwa yankin da abin ya faru domin gane wa idonsu.
Kwararru sun bayyana guguwar Daniel a matsayin mai matukar hatsari bayan da ta hallaka mutum 27 a kasashen Turkiyya, Bulgaria da Greece a yan kwanakin nan.