Ana zargin dan NYSC ya soka mahaifinsa wuka har lahira

Abin ya faru ne bayan mahaifin ya kai wa dan nasa ziyara a Abuja daga Legas, inda mahaifin ya nuna rashin amincewarsa da bakin halaye marasa kyau da ya gani daga dan nasa.

Ana zargin dan NYSC ya soka mahaifinsa wuka har lahira

Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Abuja

Wani matashi da ke aikin yi wa kasa hidima (NYSC) ya soka wa mahaifinsa wuka har lahira a unugwar Guzape da ke yankin Babban Birnin Tarayya.

Abin ya faru ne bayan mahaifin ya kai wa dan nasa ziyara a Abuja daga Legas, inda mahaifin ya nuna rashin amincewarsa da bakin halaye marasa kyau da ya gani daga dan nasa.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 11 na dare bayan dawowar dan daga kulob, inda mahaifin, wanda ke harkar kasuwancin gidaje da filaye ne, ya yi nasa tambayoyi.

Sun kara da cewa lamarin kuma yana da alaka da zargin yin facaka da kudaden kasuwanci.

A sakamakon haka aka samu sa-in-sa a tsakaninsu, inda dan ya dauko wuka ya soka wa mahaifin nasa mai suna Mista Adimike Godwin.

Daga nan ne makwabta suka sanar da jami’an tsaro, amma kafin isowar ’yan sanda dan ya tsare.

Da take tabbatar da labarin, mai magana da yawun ’yan sanda na Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan “Mutuuwar Mista Adimike Godwin a yankin Guzape, wanda muka samu labari ta hanyar kiran gaggawa.
“Jami’anmu sun je sun iske shi kwance cikin jini inda daga bayan likitoci a Babban Asibitin Karu suka tabbatar cewa rai ya yi halinsa.

“’Yan sanda sun tsare wasu mutane biyar da ake zargi ciki har da dangin mamacin kuma Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarnin a gudanar da zuzzurfan bincike,” in ji Josephine.