Pantami ya janye takararsa ta Gwamnan Gombe a APC

Janyewar na zuwa ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da kuma nazarin yadda ake shirye-shiryen zaɓen fidda gwani a jihar.

Pantami ya janye takararsa ta Gwamnan Gombe a APC

Isa Ali Pantami

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye daga zaɓen fidda gwani na gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar APC.

Pantami ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kakakin ƙungiyar Pantamiyya Movement, Barista Ibrahim M. Attahir, ya fitar.

Ya ce matakin janyewar ya biyo bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da kuma nazarin yadda ake tafiyar da shirye-shiryen zaɓen fidda gwanin kai tsaye a jihar.

Shi ma da kansa cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na soshiyal midiya, Pantami ya ce ya yi hakan ne saboda karya Dokar Zaɓe ta 2026, da kuma gazawar jam’iyyar na samar da hanyoyin sadarwa da fitar da bayanai kan zaɓen cikin gida.

Sanarwar ta ce tun da farko Pantami ya shiga takarar ne bisa roƙon shugabannin jam’iyya, matasa, mata da sauran masu ruwa da tsaki, inda ya bi dukkan ka’idojin da ake buƙata.

Haka kuma, an ce shi kaɗai ne ɗan takarar da ya halarci taron sulhu da rundunar ‘yan sanda ta shirya a Gombe, inda wakilinsa shi kaɗai ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Sai dai ƙungiyarsa ta zargi shugabannin APC da gaza samar da muhimman bayanai da suka shafi yadda za a gudanar da zaɓen fidda gwanin.

Ta ce duk da wasiƙu da aka aika na neman bayani kan tsarin zaɓe, wuraren tantance wakilai da cibiyoyin tattara sakamako, ba a ba da amsa ba.

Sanarwar ta ce rashin bin ƙa’idojin da Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada da kuma tsarin jam’iyya na iya sa a gaza tabbatar da sahihancin zaɓen.