APC ta ba Gwamna Inuwa takarar Sanatan Gombe ta Arewa

Wannan mataki na nuni da yadda jam’iyyar ke fifita tsarin yarjejeniya wajen zabar ’yan takara gabanin babban zaben 2027, tare da bayyana matakin siyasa na gaba da gwamnan zai dauka bayan kammala wa’adinsa.

APC ta ba Gwamna Inuwa takarar Sanatan Gombe ta Arewa

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya zama da takarar kujerar Sanatan Gombe ta Arewa a Jam’iyyar APC bayan fitowarsa a matsayin wanda aka amince da shi ta hanyar yarjejeniya a jam’iyyar.

Jam’iyyar ta kuma mika masa fom din takarar jam’iyyar a wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gombe.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da masu neman takarar gwamna da ’yan majalisun tarayya, mambobin Kwamitin Gudanarwa na Jiha, dattawan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki. Haka kuma, an ga Mataimakin Sakataren Kudi na Kasa na APC, Hamma Adama Ali Kumo, tare da jami’an shiyyar Arewa maso Gabas na jam’iyyar.

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya kasance shi kadai zai nemi takarar kujerar Sanata, an amince da shi baki daya a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Daga bisani, Ali Kumo tare da Shugaban APC na Jihar Gombe, Mohammed Dantata Ndus, suka mika masa fom din takara.

Wannan mataki na nuni da yadda jam’iyyar ke fifita tsarin yarjejeniya wajen zabar ’yan takara gabanin babban zaben 2027, tare da bayyana matakin siyasa na gaba da gwamnan zai dauka bayan kammala wa’adinsa.

Shugabannin jam’iyyar a wajen taron sun jaddada kudirinsu na tabbatar da hadin kai da zaman lafiya yayin da shirye-shiryen tunkarar zabukan ke kara karfi.