’Yan bindiga sun kashe fararen hula 11 a harin ramuwar gayya a Katsina

An kashe mutane 11 a wani harin ramuwar gayya da ’yan bindiga suka kai a kauyen Gwalgoro da ke Karamar Hukumar Kankia a Jihar Katsina.

’Yan bindiga sun kashe fararen hula 11 a harin ramuwar gayya a Katsina

‘Yan bindiga

An kashe mutane 11 a wani harin ramuwar gayya da ’yan bindiga suka kai a kauyen Gwalgoro da ke Karamar Hukumar Kankia a Jihar Katsina.

’Yan bindiga sun kai harin ne bayan awanni kaɗan da jami’an tsaro suka kashe wasu ’yan ta’addan tare da nasarar dakile wani hari da suka kai.

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ’yan bindigar sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da wani shahararren jagorn ’yan bindiga mai suna Mohammadu Fulani yake jagorantar su zuwa manyan gadoji a Karamar Hukumar Kankia da nufin aikata laifi.

Kwamishinan Tsaro na jihar, Nasiru Mu’azu, ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa tare da yin Allah wadai da harin.

Da aka samu wannan bayani, al’ummar yankin suka sanar da jami’an tsaro, inda DPO na Kankia ya tattara jami’an tsaro kuma suka yi nasarar dakile harin.

Jami’an tsaro sun yi artabu da ’yan bindigar, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da kwato babura guda takwas da kuma shanun da aka sace, kuma suna hannun ‘yan sanda a halin yanzu.

A cewar kwamishinan, daga baya ’yan bindigar suka sake taruwa, suka kai hairn ramuwar gayya a kauyen Gwalgoro da ke cikin Gundumar Gyaza/Kunduru da misalin ƙarfe 12 na rana, inda suka kashe mazauna kauyen goma sha ɗaya a abin da gwamnati ta bayyana a matsayin “mugun hari kan fararen hula marasa laifi.”

Gwamnatin jihar ta tir da kisan, tana mai bayyana kai wa fararen hula hari a matsayin abin da ba za a taɓa yarda da shi ba kuma aikin ta’addanci ne.

Ta kuma yaba da gaggawar jami’an tsaro wajen dakile harin farko, tare da ƙarfafa mazauna yankin da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da kuma bayar da bayanai cikin lokaci ga jami’an tsaro.

Haka kuma ta tabbatar da kudirin gwamnati na ci gaba da yaki da rashin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.