APC ta tabbatar wa Gwamna Inuwa Yahaya takarar sanata a Gombe
Kwamitin ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa tsarin da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jam’iyyar ya tanada.
Gwaman Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya
Jam’iyyar APC ta tabbatar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, DCP Mohammed Ahmed mai ritaya da Jerry Joseph Damara a matsayin ’yan takararta na Sanata a Jihar Gombe gabanin Zaɓen 2027.
Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na APC a jihar, Mallam Labiru Musa Kafur, ya ce zaɓen kai tsaye da aka gudanar a ƙananan hukumomi 11 na jihar ya gudana cikin lumana da gaskiya.
- EFCC ta kama tsohon Ministan Lantarki Saleh Mamman
- Yadda aka yi zargin ina son kashe Tinubu domin na karɓi mulki — Shettima
A sakamakon da aka bayyana, Inuwa Yahaya ya zama ɗan takarar Sanatan Gombe ta Arewa bayan samun ƙuri’u 131,009, yayin da DCP Mohammed Ahmed mai ritaya ya lashe tikitin Gombe ta Tsakiya da ƙuri’u 89,415.
Haka kuma, Jerry Joseph Damara ya zama ɗan takarar APC na kujerar Sanatan Gombe ta Kudu bayan samun ƙuri’u 56,687.
Kwamitin ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa tsarin da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jam’iyyar ya tanada, tare da bai wa mambobi damar zaɓar ’yan takararsu kai tsaye.
Kafur ya yaba wa shugabannin jam’iyya, jami’an tsaro da kafafen yaɗa labarai bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar zaɓen.