Arsenal ta lashe Firimiyar Ingila karo na farko cikin shekaru 22

A yanzu Arsenal tana da maki 82 yayin da City da ke biye ta haɗa maki 78 cikin wasanni 37 a bana.

Arsenal ta lashe Firimiyar Ingila karo na farko cikin shekaru 22

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lashe gasar Firimiyar Ingila ta bana wadda ita ce karon farko cikin shekaru 22.

Nasarar da Arsenal ta samu na zuwa ne bayan Manchester City ta yi kunnen doki 1–1 a wasan mako na 37 da ta fafata da Bournemouth.

Wannan sakamakon na ranar Talata ya bar ƙungiyar da Mikel Arteta tana jan ragama da tazarar maki huɗu a saman teburi kafin wasannin ƙarshe na kakar da za a buga ranar Lahadi.

A yanzu za a miƙa wa Arsenal kofinta a ranar Lahadi, a lokacin da za ta buga wasan ƙarshe bana tsakaninta da Crystal Palace.