Atiku zai ziyarci Amurka kan matsalar tsaro da tattalin arziki a Najeriya

Ya yi watsi da zargin cewa neman goyon bayan ƙasashen waje manufa ce ta gayyato waɗanda za su yi wa Najeriya katsalandan.

Atiku zai ziyarci Amurka kan matsalar tsaro da tattalin arziki a Najeriya

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai ziyarci ƙasar Amurka domin jawo hankalin ƙasashen duniya dangane da matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin jagoranci nagari da ke addabar Najeriya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, a yayin ziyarar, Atiku zai gana da masu tsara manufofi da manyan cibiyoyi domin tattauna abin da ya bayyana a matsayin “matsalolin cikin gida” da ya ce ba za a yi watsi da su ko siyasantar da lamarinsu ba.

Ya ce hare-haren ’yan ta’adda a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, zuwa tashin-tashinar zubar da jini a yankin Tsakiyar Najeriya, da kuma yawaitar satar mutane da miyagun laifuka, duk suna nuni da yadda ƙasar ke fuskantar matsanancin ƙalubale wajen kare rayuka da dukiyoyi.

“Atiku ya yi gargaɗin cewa Najeriya na rasa ikon sauke mafi muhimmancin nauyin da ya rataya a wuyanta, wato kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji sanarwar.

Haka kuma ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki, durƙushewar darajar kuɗi sun jefa miliyoyin ‘yan ƙasar cikin matsin rayuwa, yayin da rashin daidaiton manufofi ke ci gaba da lalata amincewar jama’a ga tattalin arzikin ƙasar.

Dangane da matsalar tsaro kuwa, Atiku ya ce lamarin ya kai matakin intaha da ya zamanto wata babbar matsala mai nasaba da rashin tsarin gwamnati wadda kuma ta jefa ’yan ƙasar cikin ƙunci mara misali,

A yayin da ya koka kan yadda al’umma ke fuskantar hare-hare da lalata musu duk wasu hanyoyin samun wata moriya ta rayuwa, Atikun ya yi gargaɗin cewa duk wata gwamnati da ta gaza tabbatar da tsaro, to kuwa tabbas ta rasa duk wata hujja ta ci gaba da riƙe madafun iko.

Da yake mayar da martani kan ziyarar da zai kai ƙetare, Atiku ya ce faɗin gaskiya kan halin da ƙasa ke ciki ba rashin kishin ƙasa ba ne, inda ya yi watsi da masu zargin cewa neman goyon bayan ƙasashen waje manufa ce ta gayyato waɗanda za su yi wa ƙasa mai ’yanci katsalandan a cikin harkokinta.

Ya jaddada cewa duk da cewa ‘yan Najeriya ne kaɗai za su zaɓi shugabanninsu, ƙasashen duniya na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kula da zaman lafiya, ingantaccen shugabanci da dimokuraɗiyya, musamman ga ƙasa mai muhimmanci kamar Najeriya.

A ƙarshe, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta daina nuna halin ko-in-kula kan nauyin da rataya a wuyanta, saboda a cewarsa ‘yan Najeriya na buƙatar ganin sakamako ba a yi ta ba su uzuri ba.

Ya kuma kira ga al’umma da su kasance masu lura da al’amuran ƙasa tare da dagewa wajen an tabbatar da gaskiya da riƙon amana, yana mai cewa sauyi na gaskiya na fitowa ne daga haɗin kan jama’a.