Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu
El-Rufai ya ce sun raba jiha da tsohon abokinsa Nuhu Ribadu da kuma Gwamnan Kaduna mai ci kuma magajinsa, Uba Sani, yanzu duk ba abokansa ba ne

Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ƙaryata zargin da tsohon abokinsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2031.
A wata hira da aka yi da El-Rufai cikin dare ne tsohon gwamnan Kadunan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu yana da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.
A yayin hirar da aka yi da shi a cikin dare a kafar Arise TV ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana cewa sun raba jiha da tsohon abokin nasa Nuhu Ribadu da kuma Gwamnan Kaduna mai ci kuma magajinsa, Sanata Uba Sani, yanzu duk ba abokansa ba ne.
Amma martaninsa, a cikin sakon da ya fitar jim kaɗan da ta tsohon gwamnan, Nuhu Ribadu ya ce, ƙarya El-Rufai yake yi cewa ya taɓa yin maganar tsayawarsa takarar 2031 da tsohon gwamnan ko da wani.
- NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?
- Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba ni muƙamin Minista — El-Rufai
“Ba don kada in yi shiru a ɗauka maganar El-Rufai gaskiya ba ce, da na yi watsi da shi. Ni tulin aikin da ke gabana a yanzu ma kaɗai ya ishe ni, balle in tsaya ɓata lokaci ina cacar baka da El-Rufai ko waninsa a kafofin watsa labarai.
Martanin Nuhu Ribadu ga El-Rufai
“Duk da cewa ya sha takala ta da caccaka ta, amma saboda mutunta tsohuwar abotarmu, ban taɓa fitowa na aibata shi ba, kun ba zan fara ba.
“Amma ina roƙon jama’a su yi watsi da maganganun da El-Rufai ya yi a kaina.
“Domin kawar da shakku, babu mahalukin da na taɓa magana da shi cewa zan nemi takarar shugaban ƙasa a 2031. Abun da na sa a gaba shi ne ganin Najeriya ta bunƙasa da kuma nasarar Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Saboda haka ina roƙon El-Rufai ya ƙyale Ni in fuskanci aikin yi wa kasa hidima da ke gabana, kamar yadda ni ma ban shiga masa harkokinsa ba.”