Ba za mu bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba — Trump

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tashin hankali da rikicin siyasa tsakanin Amurka da Iran, lamarin da ke ɗaukar hankalin ƙasashen duniya.

Ba za mu bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba — Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce gwamnatin su na tattaunawa da Iran domin cimma wata yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu.

Trump ya bayyana cewa, Amurka za ta cimma abin da take buƙata “ta kowace hanya,” yana mai jaddada cewa, ba za a bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tashin hankali da rikicin siyasa tsakanin Amurka da Iran, lamarin da ke ɗaukar hankalin ƙasashen duniya.

Sai dai har yanzu Iran ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan sabon furucin na Trump ba, yayin da masu lura da al’amuran siyasa ke ganin matakin na iya buɗe ƙofar ƙarin tattaunawa tsakanin ɓangarorin.