Baba-Ahmed ya nemi El-Rufai ya mayar da hankali kan zarge-zargen da ake masa
El-Rufai dai na hannun EFCC inda ta ke bincike kan wasu zarge-zarge a kansa.
Hakeem Baba-Ahmed, Tsohon Mai Bai Wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa, ya buƙaci Nasir El-Rufai ya daina ƙara ɓallo rikici, maimakon haka ya mai da hankali wajen fuskantar zarge-zargen da ake masa.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels, Baba-Ahmed ya ce zai fi dacewq El-Rufai ya ɗauki dangana tare da mayar da hankali kan amsa zarge-zargen rashawa da suka shafi lokacin mulkinsa.
- Gwamnatin Kano ta rufe gidajen gala ta kuma haramta kiɗan DJ
- An kashe kwamandan ISWAP Abou Aisha a Borno
Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da takun saƙa da nemo sabbin rikice-rikice na iya ƙara jefa shi cikin matsaloli.
Ya kuma ce batun yin kutse a wayar Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu sun ƙara jefa shi cikin matsala.
A cewarsa, El-Rufai zai fi dacewa ya yi amfani da jam’iyyar ADC wajen warware batutuwan da ake zarginsa da su, maimakon shiga wasu sabbin rikice-rikice.
Kalaman tsohon gwamnan sun tayar da ƙura, yayin da yake hannun EFCC inda ta ke gudanar da bincike a kansa.