Babbar Sallah: Sarkin Musulmi ya ba da umarnin duba watan Zul-Hajji
Sarkin Musulmi ya ba da umarnin a fara duba watan Zul-Hajji 1447 daga gobe Lahadi 17 ga watan Mayu 2026 daidai da 29 ga Zulƙida 1447 Hijiriyya.
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba watan Zul-Hajji, watan Sallah babba.
A wata sanarwar da Shugaban Kwamitin bayar da Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci na majalisar Sarkin Musulmi kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya fitar, ya ce Sarkin Musulmi ya ba da umarnin a fara duba watan Zul-Hajji 1447 daga gobe Lahadi 17 ga watan Mayu 2026 daidai da 29 ga Zulƙida 1447 Hijiriyya.
Sarkin Musulmi ya buƙaci duk wanda ya ga wata ya sanar da hakimi ko uban ƙasa na kusa da shi don sanar da Majalisar Sarkin Musulmi.
Watan Zul-Hajji, wanda a cikinsa ake yin Babbar Sallah da kuma aikin Hajji, yana da muhimmanci ga al’ummar Musulmi.
- Abin Al’ajabi ya janye daga neman takarar Majalisar Tarayya
- ICPC ta hana El-Rufai samun magani da abinci —Iyalinsa
Watan yana tattare da wasu ladubba a ayyukan ibada da ake buƙatar Musulmi ya aiki, musamman a kwanaki 10 na farkon wata.
Daga ciki akwai yawaita zikiri da kuma yin azumi a kwanaki 9 na farkon watan, sannan a yi hakan Idin Babbar Sallah a ranar 10 ga wata.
Haka ma akwai ladubba da ake buƙatar wanda zai yi Layya, kar ya aikata bayan shigowar watan Zul-Hajji kamar yankan farce da aski da sauransu.
A cikin watan ne kuma Alhazai suke yin tsayuwar Tafa a ranar Tara ga wata, inda suke komawa su kwana a Filin Muzdalifa, sannan washegari ranar Babbar Sallah su yi jiran farko da yanka Hadaya da aski da Ɗawafin Aikin Hajji.