CAF ta fitar da jadawalin AFCON 2027

Har yanzu ba a bayyana ƙasar da za ta buɗe da kuma rufe gasar ba a tsakanin Uganda da Kenya da Tanzaniya.

CAF ta fitar da jadawalin AFCON 2027

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afirka CAF ta sanar da cewa gasar cin kofin nahiyar (AFCON) za ta gudana daga 19 ga Yuni zuwa 17 ga Yulin 2026 a ƙasashen Yuganda da Kenya da kuma Tanzaniya.

CAF ta ce fitar da jadawalin na zuwa ne bayan amincewar da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ta yi a taron da aka yi a birnin Vancouver na ƙasar Canada.

Sai dai har yanzu ba a bayyana ƙasar da za ta buɗe da kuma rufe gasar ba a tsakanin Yuganda da Kenya da Tanzaniya.

Shugaban hukumar CAF, Patrice Motsepe, ya ce shirye-shirye na tafiya yadda ya kamata, yana mai nuna ƙwarin gwiwar cewa gasar za ta yi nasara.

Wannan ne dai karon farko da za a shirya wasannin AFCON da ƙasashe uku tare, haka nan na farko da za a gudanar a yankin gabashin Afirka, tun bayan wacce aka gani a shekarar 1976 a ƙasar Habasha.