DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani ke neman kawar da na Hausawa

Sunaye irin su Talle da Danliti da Hausawa ke amfani da su a da can baya na neman bacewa, yayin da sunayen zamani ke neman maye gurbinsu. Ko wadanne dalilai ne suka sa hakan?

DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani ke neman kawar da na Hausawa

AI generated image

A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su.

Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa  ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su.

Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a al’adance da ma a addinance?

Amsoshin wadannan da ma wasu tambayoyi makamantansu shirin Daga Laraba na wannan makon zai binciko

Domin sauke shirin, latsa nan

Amurka za ta sayar wa Saudiyya makaman dala biliyan 1.96

Majalisar Ukraine ta amince da sabuwar gwamnati

Salihu Lukman ya fice daga Jam’iyyar ADC

Kotu ta hana FRSC tare motoci a titunan Kano