DAGA LARABA: Shin Ya Dace A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?

Muhawara na kara kaurewa kan biyan kudin fansa ga masu satar mutane don kuɗin fansa. Yayin da wasu ke ganin bai kamata ba, wasu kuwa nasu tunanin daban.

DAGA LARABA: Shin Ya Dace A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?

’Yan daban daji

A cikin ’yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.

A duk lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, ’yan uwansu kan shiga tsaka mai wuya tsakanin biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko kuma tsayawa da hukumomin tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi.

Shin ko ya kamata al’umma su ci gaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ’yan uwansu?

Wannan shi ne batun da shirin Najriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan