DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai
Matsalar tsaro da taki-ci taki cinyewa na da nasaba da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba musamman a yankin Arewacin Najeriya, kamar yadda masana suka bayyana.
Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare.
Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro.
‘Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai.
- NAJERIYA A YAU: Daga Alƙawari Zuwa Mulki, Yadda Siyasa Ke Sauya Manufa
- DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah
Shirin Daga Laraba na wannan makon, bincike ne kan yadda ‘yan ta’adda ke amfani da albarkarun kasa na zinare wajen siyan makamai a yankin arewa maso yamma.
Domin sauke shirin, latsa nan