Dalilin da muka hana Obi da Kwankwaso tikitin takara — PRP

Duk da rashin cimma matsaya tsakaninsu jam’iyyar da su Kwankwaso, ɓangarorin biyu sun rabu cikin lumana.

Dalilin da muka hana Obi da Kwankwaso tikitin takara — PRP

Shugaban jam’iyyar PRP, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana dalilin da ya sa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ba su shiga jamiyyar ba a yayin da Zaɓen 2027 ya gabato.

Ya ce tattaunawar da aka yi da su ta rushe ne bayan sun buƙaci a ba su tikitin takarar shugaban ƙasa kai tsaye ba tare da an yi zaɓen fidda-gwani ba a jam’iyyar.

Da yake magana a shirin siyasa na Hausa a DITV Kaduna, Baba-Ahmed ya ce PRP ta ƙi amincewa da hakan, tana mai cewa dole ne duk mai shiga jam’iyyar ya bi tsarin dimokuraɗiyyarta.

Ya ce an shawarce su da su fara shiga jam’iyyar sannan daga baya su nemi takara kamar yadda aka bai wa kowa dama.

A cewarsa, an kuma tattauna batun rabon muƙamai ga magoya bayan su, sai dai PRP ta ce hakan ba matsala ba ce idan sun riga sun zama halastattun mambobi.

Shugaban PRPn ya ƙara da cewa akwai tabbatar akwai wata ’yar damuwa da suka shafi rikice-rikicen cikin gida da kuma matsayin jam’iyyar a wurin Hukumar Zaɓe ta INEC, amma an fara magance su.

Ya ce duk da rashin cimma matsaya tsakaninsu jam’iyyar da su Kwankwaso, ɓangarorin biyu sun rabu cikin lumana ba tare da wata matsala ba.