Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi

Muhuyi ya ce an bayar da belinsa, tare da buƙatar ya koma Abuja a ranar Laraba.

Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi

Tsohon Shugaban Hukumar Kaɓar Koke-koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama shi.

Ya ce an kama shi ne saboda jagorantar shari’ar almundahanar biliyoyin Naira na Dala Inland Dry Port, wadda ta shafi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da iyalinsa.

Muhuyi, ya shaida wa DCL Hausa cewa an tafi da shi Abuja cikin dare.

“Da aka kama ni, suka sanya jami’ai biyu ɗauke da bindiga a gefena, sai wasu uku a gaba. Haka muka tafi daga Kano zuwa Abuja cikin dare,” in ji shi.

Ya ce ’yan sandan sun ƙi nuna masa takardar izinin kama shi har sai da suka isa Abuja.

“Da muka isa, suka gabatar min da sabbi  tuhume-tuhume na ɓatanci da kutse.

“A ina ne wanda ake zargi zai ki kare kansa ya kuma umarci ’yan sanda su kama babban lauya mai shigar da ƙara?” ya tambaya.

An bayar da belinsa, amma an umarce shi da ya koma Abuja a ranar Laraba tare da miƙa fasfo d5insa.

Ganduje da ’ya’yansa na fuskantar shari’a kan zargin canja mallakar kaso 20 a aikin Dala Inland Dry Port ba bisa ƙa’ida ba.