Dorinar ruwa ta kashe mutum 2, ta jikkata 6 a Gombe
Al’ummar yankin sun nuna damuwa matuƙa kan yadda dabbar ta addabe su.
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki.
Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa.
- Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum
- Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki
Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki.
Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.”
A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi mai suna Sama’ila Garba (Mai Lasa), bayan ya faɗa cikin ruwa.
Shaidu, sun ce dabbar ta yi ƙoƙarin kashe matashin, ta yadda hanjin cikinsa sai da ya fito, kafin a ceto shi.
Garba Zafi, ɗan uwansa, ya ce Sama’ila ya je bakin ruwa ne kawai sai ya ji ya faɗa, daga nan Dorinar ta afka masa.
Wani mazaunin garin, Akilu Gyara Sa’a, ya roƙi gwamnati ta kai musu agaji duba da yadda rayuwar mutane ke da muhimmanci.
Ya ce: “Dorinar tana lalata gonaki, tana kashe mutane. Gwamnati ta hanzarta magance matsalar kafin abin ya ta’azzara.”
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce zai bincika domin samun cikakken bayani kan lamarin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske kan lamarin ba.