DSS ta gurfanar da El-Rufai kan zargin yin kutse a wayar Ribadu

El-Rufai, ya musanta zargin da ake masa bayan an karanta masa tuhume-tuhumen a kotu.

DSS ta gurfanar da El-Rufai kan zargin yin kutse a wayar Ribadu

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

An gurfanar da shi ne bisa zargin yin kutse a wayar Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu.

DSS ta ce El-Rufai ya yi kutse a wayar Ribadu ba bisa ƙa’ida ba, wayarsa Muhimman Abubauwan Da Suka Shafi Ƙasa.

A cewar DSS, El-Rufai ya bayyana haka ne da bakinsa yayin hira a gidan talabijin na Arise TV a Abuja ranar 13 ga watan Fabrairu.

Masu gabatar da ƙara, sun bayyana cewa hakan ya saɓa wa sashe na 7 (b) da (c) na Dokar Kare Muhimman Kayan Sadarwar Ƙasa ta shekarar 2024, kuma laifin yana da hukunci ƙarƙashin sashe na 5 (1) na Dokar Laifukan Intanet ta 2024.

El-Rufai, ya musanta zargin da ake masa bayan an karanta masa tuhume-tuhumen a kotu.

Lauyan DSS, Oluwole Aladedoye (SAN), ya roƙi kotu da ta ba su kwanaki uku domin gabatar da shaidu kafin ci gaba da shari’ar.

Tun da farko, lauyan ya sanar da kotu cewa an yi wa tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamman gyara zuwa inda aka mayar da su guda biyar.

A nasa ɓangaren, lauyan El-Rufai, Oluwole Iyamu (SAN), ya ce wanda yake karewa yana hannun Hukumar ICPC, ya kamata kotu ta yi la’akari da buƙatar ba da shi beli da suka shigar tun ranar 17 ga watan Fabrairu.

Haka kuma, masu gabatar da ƙara sun roƙi kotu da ta ba da umarnin ɓoye sunaye da fuskokin shaidun da za su gabatar a shari’ar, tare da ba su damar amfani da sunayen bogi domin kare su daga barazana daga magoya bayan El-Rufai.

Sai dai lauyan masu kare El-Rufai, ya ƙi amincewa da wannan buƙata, yana mai cewa hakan zai tauye haƙƙin kundin tsarin mulki na wanda ake tuhuma na sanin waɗanda ke zarginsa.

Ya kuma ƙara da cewa babu wata hujja da ta nuna cewa El-Rufai na da wata ƙungiyar magoya baya da za ta iya razana shaidu ko tayar da hankali yayin shari’ar.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta ɗage shari’ar zuwa ranakun 18, 19 da 20 ga watan Mayu.