DSS Ta Rufe Asibiti Kan Zargin Rashin Ƙwarewa A Jos

An rufe Asibitin AL-Ihsan da ke unguwar Rogo sakamakon rasuwar wata wada ake zargin likita dan koyo ne ya yi mata tiyata

DSS Ta Rufe Asibiti Kan Zargin Rashin Ƙwarewa A Jos

Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya (DSS) ta rufe wani asibiti kan zargin wani dan koyo yana yi wa marasa lafiya tiyata a garin Jos na Jihar Filato.

An rufe Asibitin AL-Ihsan da ke unguwar Rogo ne sakamakon  rasuwar wata mata da ake zargin rashin ƙwarewar ma’aikatan asibitin ne sanadiyar rasuwarta.

Wani mazaunin unguwar, Muhammad Albasu ya shaida mana cewa “Likitan da ya yi wa matar nan da ta rasu tiyata ba ƙwararre ba ne, yanzu ma yake karatu, don haka ba ma likita ba ne, bai iya aikin ba.

“Abin da ya sa aka kai ƙarar asibitin ga hukuma ke nan, ya jima yana tiyata a asibitin kuma jama’a sun san cewa shi ba likita ba ne.”

A makon da ya gabata ne wanda ake zargin dan koyo ne ya yi wa matar tiyatar da ta zamo ajalinta.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce, inda yawancin mazauna yankin ke alakanta rasuwar da tiyatar da aka yi.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da neman ƙarin bayani game da ƙwarewar ma’aikacin da ya yi aikin tiyatar.

Wata majiya ta sanar da wakilinmu cewa an kai ƙorafi ga Hukumar Lafiya ta Jihar Filato, an kuma kai takardar neman a binciki asibitin ga DSS.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, iyalan matar da hukumar da abin ya shafa ba su ce komai dangane da batun ba.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta