DSS za ta binciki El-Rufai kan zargin odar guba —ONSA

ONSA ya bayyana cewa Hukumar Tsaro ta DSS za ta gudanar da bincike kan zargin shigo da gubar Thallium Sulphat tare da gayyatar El-Rufai da duk masu bayanai kan lamarin

DSS za ta binciki El-Rufai kan zargin odar guba —ONSA

Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro (ONSA) ya mayar da martani kan zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa na shigo da gubar Thallium Sulphate daga kasar waje.

ONSA ya bayyana cewa Hukumar Tsaro ta DSS za ta gudanar da bincike kan zargin shigo da gubar Thallium Sulphat tare da gayyatar El-Rufai da duk masu bayanai kan lamarin domin gano gaskiya.

Zargin da El-Rufai ya yi ya jawo fargaba da zargin yiwuwar amfani da gubar mai hatsarin gaske kan ’yan adawa. El-Rufai ya bayyana cewa shugabannin adawa na sane game da lamarin, kamar yadda ya bayyana a cikin wata wasika.

Kwararru sun bayyana sinadarin a matsayin guba mai  matuka hadarin gaske da ke iya kashe mutum ba tare da barin wata alama ba.

El-Rufai ya yi zargin ne bayan a wata hirar da tashar talabijin ta Arise ta yi da shi, cewa ya samu sautin waya Ribadu da aka tatsa, inda Ribadun ke ba da umarnin a kama shi.

A cewarsa, duk da cewa ya san yin hakan ya saba doka, amma akwai masu iya tsatsar bayanan gwamnati, kamar yadda ita ma take tatsar wayar jama’a.

Bayan zargin shigo da Thallium Sulphate da El-Rufai ya yi ne Ofishin NSA ta hannun Manjo-Janar OM Adesuyi, ta aike amsa da takardar neman ya gabatar da hujjoji kan zargin da ya yi na shigo da gudabar mai nauyin kilogram 10 daga kasa Polland.

Wasikar ta ce, “Lura da hadarin thallium wanda ke da doka a kansa, yana da kyau domin kare al’umma, kuma bisa ruhin dimokuradiyya da kare yardar al’ummar ka bayar da wadanna bayanai:

“3. Yawansa da kuma adadin da za a karba ko aka riga aka karba.

“5. Dokokin kula da shi na hukumomin NAFDAC, NCDC, da dokokin kare muhalli da dangoginsu.

“6. Ko akwai barazana ga rayuwar al’umma da wasu matakan kariyar lafiyar al’umma da aka tanada, lura da hadarin sinadarin.”

Takardar ta karyata labarin shigo da sinadarin ko niyyar yin haka daga gwamnati.

An gano baƙin haure 30 a ɓoye cikin tankar mai a Turkiyya

An tsare ɗan gwagwarmaya kan sukar gwamnatin sojin Nijar

Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida

Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida