Yau El-Rufai zai bayyana a ofishin EFCC

Bayan amsa gayyatar EFCC ana sa ran El-Rufai ya bayyana a ofishin Hukumar ICPC da ke Abuja domin amsa tambayoyi

Yau El-Rufai zai bayyana a ofishin EFCC

A yau Litinin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai zai bayyana a gaban Hukumar Yaƙi da masu Karya Tattalin Arzikin Ƙasa (EFCC) domin amsa tambayoyi.

El-Rufai ya bayyana haka ne bayan dambarwa tsakaninsa da jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da suka yi yunƙurin kama shi a filin jirgin sama na Abuja bayan dawowarsa Najeriya.

Ya bayyana cewa tun yana ƙasar waje EFCC ta aiko takardar gayyatar gidansa, amma lauyoyinsa suka sanar da hukumar cewa ya riga ya yi bulaguron da ya saba yi a duk ƙarshen shekara zuwa ƙasar waje, amma da zarar ya dawo zai kai kansa ofishinta domin amsa gayyatar.

A cewarsa tun kafin dawowarsa ya sanar da EFCC cewa zai bayyana a ofishinta a ranar Litinin 16 ga watan Fabrairu, wanda ya zo daidai da ranar haihuwarsa domin amsa tambayoyin da take don ta yi masa.

A ranar Alhamis jami’an DSS suka ƙwace fasfo ɗin El-Rufai a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan dawowarsa hutu daga ƙasar waje.

Jami’an sun kuma yi yunƙurin tafiya da tsohon gwamnan, amma ya buƙaci su ba shi takardar izinin yin hakan daga kotu, suka kasa.

Don haka ya ƙi bin su, kuma jama’ar da ke wurin suka yi wa jami’an ca, suka hana tafiya da shi.

Daga bisani El-Rufai ya bayyana cewa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ne ta aiko jami’an na DSS domin su kama shi ba bisa ka’ida ba, yana mai zargin hannun Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro da amfani da ICPC a matsayin karen farauta domin kama ’yan adawa.

Sai dai ya bayyana cewa daga baya ICPC ta aiko masa da takardar gayyata kuma ya amsa mata da cewa tana nan tafe bayan ya gama da EFCC.

Kawo dai babuwani bayani game da ainihin dalilin da kowanne daga cikin hukumomin yake neman yi wa El-Rufai tambayoyi.

A baya-bayan nan, tsohon Gwamnan Kadunan, wanda aka tattauna da shi a kafar Trust TV da kuma Arise, ya yi maganganu da suka tayar da ƙura a siyasar Najeriya, ciki har da zargin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribaɗu da yin odar wata gubar kisa ta Thallium Phosphate, mai hatsari, zargin da Nuhu Ribaɗu ya ƙaryata, ya kuma ƙalubalance shi da ya kawo hujja.

Gabanin haka, El-Rufai ya yi zargin Nuhu Ribaɗu da bayar da umarnin a kama shi.

Tun da farko a yayin hirarsa da Trust TV, wanda suka raba gari da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da Jam’iyyar APC, bayan an ƙi nada shi minista, ya bayyana cewa shi da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba su taɓa yin wata alaƙa ta kashin kai ba.

Ya ƙara da cewa ko da an nada shi minista ma, da ba zai daɗe ba zai bar gwamnatin.

A yayin tattaunawar da tashar talabijin ta Arise ta yi da shi daga baya, tsohon gwamnan Kaduna ya yi iƙirarin cewa ya samu bayanan sirri daga wani wanda ya tatsi sadarwar wayar Ribaɗu, inda yake bayar da umarnin a kama shi.

Iƙirarin tatsar wayar NSA ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda ake bayyana shi a matsayin daɓa wa kai wuƙa da kuma barazanar tsaron ƙasa.

Kakakin Shugaban Ƙasa, ya mayar da martani game lamarin da cewa El-Rufai zai yi bayani game da wannan iƙirarin

Sai dai wasu na ganin kalaman nasa a matsayin wani salo ta neman tilasta gwamnati ta tsare shi domin ya yi farin jini.