Gambiya za ta kwaikwayi tsare-tsaren aikin gwamnati na Najeriya

Gambiya na kallon Najeriya a matsayin “babbar ’yar’uwa”, wadda ta daɗe tana taimaka mata a fannoni daban-daban.

Gambiya za ta kwaikwayi tsare-tsaren aikin gwamnati na Najeriya

Sakataren Majalisar Ministoci kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Gambiya, Alieu Njie yayin wata ziyara da tawagar ƙasar ta kai Cibiyar Horar da Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya (PSIN) da ke Abuja.

Gwamnatin Gambiya ta bayyana aniyarta ta amfani da wasu daga cikin tsare-tsaren aikin gwamnati na Najeriya domin inganta horar da ma’aikata da tafiyar da harkokin gwamnati a ƙasar.

Sakataren Majalisar Ministoci kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Gambiya, Alieu Njie, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da tawagar ƙasar ta kai Cibiyar Horar da Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya (PSIN) da ke Abuja.

Njie ya ce Gambiya na kallon Najeriya a matsayin “babbar ’yar’uwa”, yana mai cewa ƙasar ta daɗe tana taimaka mata a fannoni daban-daban da suka haɗa da tsaro, lafiya da fasaha.

Ya ce manufar ziyarar ita ce koyon abubuwan da Najeriya ta cimma a fannin inganta aikin gwamnati domin aiwatar da makamantansu a Gambiya.

A nata ɓangaren, Shugabar PSIN, Dakta Imeh Okon, ta ce ziyarar za ta ƙara ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu tare da ba su damar musayar ƙwarewa da gogewa a fannin gudanar da aikace-aikacen gwamnati.

Ta bayyana cewa cibiyar ta gudanar da dubban jarabawar ƙarin girma ta hanyar amfani da fasaha da kuma faɗaɗa shirye-shiryen horaswa domin inganta ƙwarewar ma’aikatan gwamnati.