Gobara ta cinye gidan hakimi a Bauchi
Gidan ya ƙone ƙurmus, an yi asarar dukiya mai tarin yawa amma an yi sa’a da hatsin ne ya faru, amma ba a samu asarar rai ba
Gobara ta ƙone gidan Barden Bauchi Hakimin Ƙasar Lere, Alhaji Sulaiman Muhammad da ke unguwar Gwallaga a cikin garin Bauchi.
Sa’in Tafawa Balewa Mallam Yunusa Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa “Wannan gobara ta auku ne akamakon kawo wutan lantarki da hantsi ranar Litini 4/8/2025 lokacin Hakimin na Fadarshi dake garin Zwall.”
Mallam Yunusa ya ce, “Gidan ya ƙone ƙurmus, an yi asarar dukiya mai tarin yawa amma an yi sa’a da hatsin ne ya faru, amma ba a samu asarar rai ba, kuma babu wanda ya jikkata.
Ya bayyana cewa makwabta da zuwan jami’an sun taimaka an aka fitar da motar da ke garejin zuwa waje, amma an tafka asara.
Sa’in yace “Muna addu’ar Allah Ya Maida masa mafi alherin abin da aka rasa, Ya kuma tsare na gaba.”