Gwamnatin Gombe za ta biya tashar Dikku da Bauchi diyyar miliyan 332

Gwamnatin za ta biya diyyar ne sakamakon rushe tashar motar da ta yi.

Gwamnatin Gombe za ta biya tashar Dikku da Bauchi diyyar miliyan 332

Gwamnatin Jihar Gombe za ta kashe Naira miliyan 332 a matsayin diyya ga masu shaguna da gine-gine a tashar motar Bauchi da Dikku sakamakon rushe su da gwamnatin ta yi.

Kwmaishinan Ma’aikatar Kudi na jihar, Alhaji Muhammad Gambo Magaji ne, ya sanarwa manema labarai hakan jim kadan bayan kammala zaman majalisar dokokin a gidan gwamnati.

Ya ce tuni kwamitin da aka dora wa alhakin duba biyan diyyar suka kammala aikinsu kuma nan ba da jimawa gwamnatin jihar za ta fara biyan wadanda lamarin ya shafa.

Kazalika, an ware filin da tsohon gwamnan jihar, Abubakar Habu Hashidu, ya ware don gina kasuwa a matsayin filin da za a gina sabuwar majalisar dokokin jihar da kuma kotu.

Majalisar ta amincewa wa gwamna Jihar, Mohammed Inuwa Yahaya, ya biya diyyar Naira miliyan 358, ga wadanda suka fara gini a filin.

Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara