Gwamnatin Kano ta raba buhunan shinkafa 54,600 don Ramadan
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon buhunan shinkafa 54,600 domin rage radadin rayuwa da mazauna jihar ke fuskanta a lokacin watan Ramadan.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon buhunan shinkafa 54,600 domin rage radadin rayuwa da mazauna jihar ke fuskanta a lokacin watan Ramadan.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a ranar Asabar a titin Maganda da ke Kano, wanda ya nuna fara shirin tallafin shekara-shekara na Ramadan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Yusuf ya bayyana shirin a matsayin al’ada ta kowace shekara da nufin tallafa wa marasa galihu a cikin watan mai alfarma.
Ya ce wannan mataki zai shafi dukkan kananan hukumomi 44 na jihar da kuma wasu rukunai da aka zaɓa.
- Ramadan: Jihar Sakkwato za ta kashe N1bn kan ciyarwar azumi
- Yau El-Rufai zai bayyana a ofishin EFCC
- NAJERIYA A YAU: Yadda Muka Yi Asarar Biliyoyin Naira A Kasuwar Singa Muna Ji Muna Gani
Ya bayyana cewa jimillar motoci 91 dauke da manyan buhunan shinkafa 54,600 masu nauyin kilo 50 za a rarraba a fadin jihar.
Daga cikin wannan adadi, motoci 44 za a tura kai tsaye zuwa kananan hukumomi, yayin da sauran motoci 47 za a raba su ga kungiyoyi da mutanen da aka zaɓa domin tallafa musu a lokacin azumi.
Domin tabbatar da gaskiya da adalci, gwamnan ya sanar da kafa kwamitoci a matakin jiha da na kananan hukumomi da za su kula da isar kayan, rabawa da kuma jigilar shinkafar.