Hadejia ta cika shekaru 120 da yi wa Turawan mulkin mallaka turjiya

Za a shafe tsawon kwanaki biyu ana gudanar da taron.

Hadejia ta cika shekaru 120 da yi wa Turawan mulkin mallaka turjiya

Tsohon Birnin Hadejia na shirin gudanar da gagarumin taron tunawa da cika shekaru 120 da yi turjiya ga mamayar turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Masu ruwa da tsaki sun jaddada muhimmancin kiyaye al’adu da tarihin gargajiya domin amfanin ’yan baya.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Alhaji Usman Abdul’aziz Galadiman Hadejia, ya bayyana taron a matsayin lokaci na yin tunani mai zurfi da kuma alfahari ga al’ummar masarautar.

Ya bayyana cewa bikin, wanda Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dokta Adamu Abubakar Maje Haruna zai karɓi bakunci, zai girmama jarumtar mutanen Hadejia waɗanda suka fafata da turawan mulkin mallaka a shekarar 1906.

Galadima, ya ƙara da cewa, Masarautar Hadejia ta tsaya tsayin daka ƙarƙashin jagorancin Sarki Muhammadu Mai-Shahada, inda ta ƙi amincewa da mulkin Birtaniya.

A cewarsa, yaƙin ya kasance mai tsanani, inda sama da mayaƙan Hadejia 800 suka riga mu gidan gaskiya, ciki har da Sarkin kansa.

Haka kuma, kwamandan turawan, Kyaftin H.C.B. Phillips, ya rasa ransa a lokacin artabun.

“Wannan ba yaƙi ne kawai ba; wani muhimmin lamari ne da ya nuna jarumta, sadaukarwa, da mutunci, wanda har yanzu yake ƙara wa martabarmu daraja,” in ji shi.

Taron, wanda za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa (24 da 25 ga watan Afrilu, 2026), zai haɗa da addu’o’i na musamman ga jaruman da suka rasu, ƙaddamar da gidan kayan tarihi, ziyartar wuraren tarihi, da kuma gagarumin bikin Hawan Doki.

Ɗaya daga cikin manyan ayyukan taron shi ne ƙaddamar da wani littafi da ke ɗauke da tarihin wannan turjiya, wanda marigayi Farfesa Haruna Wakili ya rubuta, yayin da Farfesa Tijjani Muhammad Naniya zai gabatar da bitarsa.

Gwamnati ta yaba da ƙoƙarin kare al’adu

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Hon. Sagir Ahmad Musa, ya jaddada aniyar gwamnati na kare al’adu da tarihi.

“Zan iya cewa cikin ƙwarin gwiwa, gwamnatin Malam Umar Namadi na iya ƙoƙarinta wajen kare al’adu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta Jihar ta amince da ware sama da Naira biliyan ɗaya domin sake gina fadar Masarautar Hadejia, a matsayin wani babban mataki na kare tarihi.

“Wannan biki na cika shekaru 120 haɗin gwiwa ne tsakanin masarauta da gwamnati, wanda ke nuna muhimmancin rubuta tarihi da kiyaye al’adu,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa Hadejia na ɗaya daga cikin masarautun ƙarshe da suka yi turjiya ga turawan mulkin mallaka a Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa yawancin manyan masarautu, har da Daular Sakkwato, sun faɗa hannun turawa tun kusan shekarar 1903, amma Hadejia ta ci gaba da gwabzawa har zuwa yaƙin ƙarshe na 1906.

Ya bayyana taron a matsayin wata dama ta yin nazari da ɗaukar darusa daga abubuwan da suka faru a baya.

Masu shirya taron sun yi kira ga kafafen yaɗa labarai da sauran al’umma da su halarci bikin, wanda aka sanya wa taken: “Turjiyar Hadejia: Kare Addini, Tsare Mutunci da Al’adu, da Kuma Zaburar da Makoma.”

Ana sa ran taron zai janyo hankalin masana tarihi, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati, da masu sha’awar al’adu daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.