Har yanzu tafiyar ceto Najeriya na gaba — Atiku
Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, jim kadan bayan hukuncin kotun ƙoli.
Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa tafiyar adawa a Najeriya ba ta kare ba, duk da hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da shugabancin David Mark a jam’iyyar ADC.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, jim kadan bayan hukuncin kotun ƙoli.
- An kashe mutum 2 da sace wasu da shanu a Sakkwato
- SSANU da NASU za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani
Ya ce, duk da cewa hukuncin wani muhimmin mataki ne ga jam’iyyar, bai kamata a dauke shi a matsayin cikakkiyar nasara ba.
A cewarsa, har yanzu akwai aiki mai yawa a gaba wajen kokarin dawo da ƙasar kan turbar da ta dace.
Ya kuma sadaukar da nasarar ga ’yan Najeriya, yana mai cewa su ne suka nuna juriyar da ake buƙata duk da ƙalubalen siyasa da tattalin arziki.
Ya jaddada cewa, dimokuradiyya ba za ta dore ba sai idan ’yan ƙasa suna ci gaba da sanya ido a kai.