SSANU da NASU za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani

Kungiyoyin sun bayyana cewa, sun ɗauki wannan mataki ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta kasa kammala tattaunawa da su kan batun ƙarin alawus-alawus da suke nema.

SSANU da NASU za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani

Kungiyoyin malamai da ma’aikatan jami’o’i wato SSANU da NASU, sun ayyana yajin aiki na ƙasa baki ɗaya wanda zai fara daga ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu, 2026.

Kungiyoyin sun bayyana cewa, sun ɗauki wannan mataki ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta kasa kammala tattaunawa da su kan batun ƙarin alawus-alawus da suke nema.

A wata wasiƙa da shugabannin ƙungiyoyin suka aika wa Ministan Ilimi, sun ce duk da cewa, an janye wata takarda da ta janyo ce-ce-ku-ce a baya, har yanzu ba a cimma matsaya kan buƙatunsu ba.

Sun ƙara da cewa, rashin gabatar da wani sabon tayin daga gwamnati ya sa dole suka ɗauki matakin shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani.

ƙungiyoyin biyu sun jaddada cewa, yajin aikin zai ci gaba har sai an warware matsalolin da suka shafi walwalar ma’aikatansu.