Hausawa sun zargi ’yan kabilar Kutep da kashe musu mutane a kauyen Taraba
Sai dai ‘yan kabilar ta Kutep sun musanta kai harin
Al’ummar Hausawa mazauna garin Takum da ke Jihar Taraba sun zargi dakarun sa–kai na ’yan kabilan Kutep da halaka musu mutane masu yawa a ranar Lahadi.
Wani Bahaushe mai suna Yakubu Sani, ya shaida wa wakilinmu cewa dakarun wadanda ke dauke da manyan makamai sun kai hari a anguwannin Hausawa da ke garin na Takum wanda ke Kudancin Jihar Taraba.
- Mutanen Daura sun shirya wa Buhari gagarumar tarba ranar da zai bar mulki
- NAJERIYA A YAU: Shin Sabuwar Gwamnati Za Ta Iya Hada Kan ’Yan Najeriya?
Ya yi zargin an halaka musu sama da mutum 15 yayin farmakin.
Ya kara da cewa ko kadan mutanensu ba su tsokani wani ba ko kuma wata kabila a yankin wanda zai sa a kai masu hari har a hallaka masu mutane.
Yakubu ya kuma ce su Hausawa ba su cikin rigimar da ke tsakin ’yan kabilar Kutep da Fulani, amma sai ga shi an huce hushi a kan su.
Yakubu ya ce dakarun sa-kai na ’yan kabilan Kutep sun kashe Hausawa matafiya 13 a kan hanyar Takum zuwa Maraba da kuma hanyan Takum zuwa Kashinbila.
Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Shugaban kungiyar ’yan kabilar Kutep na kasa, Emmanuel Ukwen ya ce yana Jalingo, babban birnin Jihar, kuma bai san abin da ke faruwa a garin na Takum ba
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar, SP Usman Abdullahi ya bayyana wa wakilinmu cewa ’yan kabilar Kutep sun kashe Hausawa biyu, wanda hakan ya harzuka Hausawa kuma rigima ya tashi a garin na Takum.
Kakakin ya kuma ce tuni aka tura sojoji da ’yan sanda a garin na domin kawo karshen rigimar