‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum
Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya.
Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su.
- An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna
- Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore
Majiyoyin da ke kauyen na sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa wadanda suka mutun sun hada da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu.
Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce ya gano faruwar hakan ne a lokacin da ya ziyarci gidan da sanyin safiyar Talata inda ya tarar da gidan gaba daya ba a halin da aka saba gani ba.
“Na zo da misalin karfe 7:00 na safe na yi ta buga kofar gidan amma babu wanda ya amsa, sai na shiga damuwa kuma daga karshe dole na balle kofar, a lokacin ne na ga gawarwakinsu a kwance a cikin dakin,” in ji shi.
Ya kuma ce, “Bayan gano lamarin nan da nan na sanar da hukumomin ’yan sanda da ma’aikatan lafiya yadda ba tare da bata lokaci ba suka ziyarci wurin inda suka tabbatar da mutuwar dukkan ’yan uwan hudu.
“Daga baya an kwashe gawarwakin zuwa babban asibitin garin Marama, inda aka ajiye su a dakin ajiyar gawarwaki domin adanawa da kuma tantance musabbabin mutuwar su.
Mutanen kauyen sun bayyana lamarin a matsayin abin da ya dame su kuma sun ce mamatan kafin nan ba su nuna alamun wata rashin lafiya ko damuwa ba kafin mutuwarsu ta farar daya.
Sun ce binciken farko da aka yi a wurin ya nuna babu wani alamun tashin hankali, amma mazauna yankin na zargin yiwuwar kamuwa da guba ko shakar gurbatacciyar iska daga wani injin janareta da suke amfani da shi.
Rundunar ’Yan Sandan jihar ta bakin Kakakinta, ASP Nahum Daso ta ce tuni an fara bincike don gano ainihin musabbabin mutuwar mutanen.