HOTUNA: Yadda aka Karrama ma’aikata da abokan huldar kamfanin Media Trust
Kamfanin ya karrama ma’aikatansa da abokan huldarsa da suka yi zarra a shekarar 2023
Kamfanin Media Trust — masu Aminiya da Daily Trust da Trust TV da kuma Trust Radio — ya karrama ma’aikatansa da suka nuna bajinta da kuma abokan huldarsa da suka yi zarra a shekarar 2023.
Kamfanin ya kuma karrama ma’aikatansa da suka shafe shekara 20, shekaru 15 da kuma shekaru 10 a wani kasaitaccen biki da ya shirya domin jinjina musu da kuma mika musu kyaututtuka.
Kamfanin ya kuma karrama ma’aikatansa da suka shekara 20 da masu 15 da kuma 10 suna aiki da shi da kyaututtukan kudi da kuma takardar shaidar yabo bisa gudummawar da suka bayar ga ci gaban kamfanin.
Gwamnatin Jihar Borno, ita ce ta lashe kambun Gwarzuwar Abokiyar a bangaren hukumomin gwamnati, sai Bankin Zenith a bangaren kamfanonin masu zaman kansu.
A yayin bikin an ba da kyaututtuka masu tsoka ga ma’aikatan kamfanin da suka zama gwaraza a bangaren rikon amana, hazakar aiki, kirkira da dai sauransu.
Ga hotunan yadda bikin ya gudana a babban ofishin kamfanin da ke Abuja:
Mahalarta taron suna tafi a lokacin da ake bayyana sunayen wadanda suka lashe kyauttuka a bikin da aka gudanar ranar Labara a hedikwatar Rukuncin Kamfanin Media Trust da ke AbujaShugaban Kamfanin Media Trust, Kabiru Yusuf, a lokacin da ake jawabi a wurin taron.Shugabar Shahen Gudanarwa da Jin Dadin Ma’aikata a Kamfanin Media Trust, Hajiya Hadiza Bala, a lokacin da ake jawabi a wurin taron.(Daga dama) Babban Edita kuma Daraktan Shashen yada Labaran Zamani na Rukunin Kamfanin Media Trust, Naziru Mika’il Abubakar da Shugaban Trust TV, Ibrahim Shehu da kuma Mukaddashin Babban Jami’in Gudanarwa na Rukunin Kamfanin Media Trust, Ibrahim Shekarau a wurin bikin.Wani sashe na kwamitin Daraktocin Rukunin Kamfanin Media Trust a wurin taron da aka gudanar a babban ofishin kamfanin da ke Abuja.(Daga hagu) Malam Abacha, wakiliin Gwamna Babagana Zulum na Jibar Borno, Wakilin Shugaban Bankin Zenith Dr. Ebenezer Onyeagwu, Group Managing Director/CEO da kuma mambobinn kwamitin daraktocin kamfanin Media TrustWakilan Gwamnatin Borno da Bankin Zenith suna gaisawa a wurin bikinFuskokin wasu daga cikin ma’ikatan da aka karrama saboda shafe akalla shekaru 10 suna aiki da kamfanin Media TrustWani sashe daga cikin ma’ikatan Rukunin Kamfanin Media Trust da aka karrama saboda shafe akalla shekaru 10 suna aiki da shiWadanda aka karrama saboda dadewa suna aiki a Rukunin Kamfanin Media Trust na akalla shekaru 10 suna aiki daA hannun dama, Hassan Alpha, wadda aka Karrama da Kyauyar Rikon Amana na Rukunin Kamfanin Media Trust na 2023Malam Abacha, wakilin Gwamna Babagana Zulum na Jibar Borno, a lokacin a shugaban kwamitin daraktocin kamfanin Media Trust ke mika masa kyautar da gwamnatin jihar ta lashe a matsayin hukumar gwamnati da huldarsa da Media Trust ta fi karfi a 2023.Wakilin Shugabna Bankin Zenith, a lokacin a shugaban Rukunin Kamfanin Media Trust, Malam Kabiru Yusuf ke mika masa kyautar da bankin ya lashe a matsayin kamfani mai zaman kansa da huldarsa da Media Trust ta fi karfi a 2023.
Wasu daga cikin mahalarta taron
Wani sashe na maharta bikinMataimakin Editan Jaridar Aminiya, Isiyaku Muhammed, ya lashe kambum Ma’aikacin Mafi Rikon AmanaAn karrama Ayuba Iliya na bangaren Trust TV da Kyauyar kwarewar aikiSagir Ibrahim shi ne ya lashe kyautar ma’aikaci mai kirkira na 2023 na kamfaninNura na sashen tallace-tallace na daga cikin wadana aka karrama saboda shafe shekaru 15 suna aikin a kamfaninWadanda aka karrama saboda shafe akalla shekaru 10 suna aiki da Rukunin Kamfanin Media TrustAn karrama Editan Dail Trust Sashen Intanet, George Taiwo da kyautar nagartar aiki.Hassana Alfa a lokacin da take karbar kyautar karramawa a matsayin Ma’aikaciya Mai Rikon Amana na Media Trust na 2023Simon Ekankan na daga cikin wadana aka karrama saboda shafe sama da shekara 10 suna aiki da kamfanin