Hukumar Alhazai ta ayyana ranar soma jigilar maniyyatan Kano
An zaɓi kamfanin jirgin sama na Max Air domin gudanar da jigilar maniyyatan Jihar Kano.
Wasu maniyyata Aikin Hajji
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ayyana 14 ga watan Mayun 2026, a matsayin ranar da za a fara jigilar maniyyata daga jihar zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Sulaiman A. Dederi, ya fitar, a ranar Lahadi.
- Harin Boko Haram ya laƙume rayuka 24 a sansanin sojin Chadi
- Rikici ya kunno kai NDC a Kano bayan komawar Kwankwaso
Sanarwar ta ambato shugaban hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle, yana bayyana hakan a yayin rufe taron bitar aikin Hajji da aka gudanar a Makarantar Sakandiren Koyar da Larabci ta SAS da ke Kano.
Ya ce an zaɓi ranar ne bayan da Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta fitar da jadawalin jigilar maniyyata, inda ya ƙara da cewa an zaɓi kamfanin jirgin sama na Max Air domin gudanar da jigilar maniyyatan jihar.
Matawalle ya tabbatar da cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin ganin an kwashe maniyyatan cikin ƙoshin lafiya da tsari.
Hukumar ta kuma buƙaci maniyyatan da su ci gaba da nazarin abubuwan da aka koyar da su, domin fahimtar yadda za su gudanar da ibadar Hajji yadda ya kamata, ta yadda za ta kasance karɓaɓɓiya.
Hakazalika, an ja hankalinsu da su tabbatar sun bi dokoki da ƙa’idojin da ƙasashen Saudiyya da Najeriya suka gindaya dangane da aikin Hajjin bana.
Aminiya ta ruwaito yadda a ranar Lahadin da ta gabata aka fara jigilar maniyyata a ƙasar, inda aka fara da maniyyata 474 daga Jihar Kogi, waɗanda suka tashi daga Filin Jirgin Sama na Abuja, yayin bikin da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya halarta.