Rikici ya kunno kai NDC a Kano bayan komawar Kwankwaso
Mai Riga ya kuma zargi shugabancin jam’iyyar na kasa da dakatar da taron zaben shugabannin jiha a Kano domin bai wa Kwankwaso damar karbe iko
Tambarin Jam’iyyar NDC
Sabuwar rigima ta kunno kai a Jam’iyyar NDC a Jihar Kano, inda shugaban Jam’iyyar, Usaini Isa Mai Riga, ya lashi takobin hana bangaren tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Kwankwaso, karbe jagorancin jam’iyyar.
Mai Riga ya bayyana haka ne, a yayin da yake zargin neman ya mika ragamar jam’iyyar ga tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar NDC a ranar Lahadi tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi.
Shigowar Kwankwaso NDC ya tayar da hankula a reshen Jihar Kano na jam’iyyar, inda Mai Riga ya nace cewa shugabancin da ke akwai ba zai mika iko ba ga bangaren jagoran na tafiyar Kwankwasiyya ba.
Mai Riga, a wata hira da ya yi da tashar Premier Radio a Kano, ya bayyana cewa taruka biyu da aka yi domin shigar da Kwankwaso jam’iyyar sun rushe saboda rashin jituwa kan tsarin shugabanci.
- ’Yan majalisa 17 sun fice daga ADC zuwa NDC
- Juyin mulki: Mutum 2 sun amince sun san da shirin kifar da gwamnati
- Kotu ta rushe zaɓen shugabannin ADC na Adamawa
“Yana so mu mika masa dukkan jam’iyyar, duk da irin sadaukarwar da muka yi lokacin da jam’iyyar ba ta da karfi ko suna,” a cewarsa, yana mai alkawarin bijirwa wa duk wani yunkuri na kifar da shugabannin yanzu.
“Wannan ba zai taba faruwa ba. Za mu bi dukkan hanyoyin doka domin tabbatar da cewa ba a kwace tsarin jam’iyyar ba,” in ji shi.
Mai Riga ya kuma zargi shugabancin jam’iyyar na kasa da dakatar da taron zaben shugabannin jiha a Kano domin bai wa Kwankwaso damar karbe iko, duk da cewa an gudanar da irin wannan taro a sauran jihohi.
Ya ce: “An umarce mu da kada mu gudanar da taron saboda shirin mika tsarin jam’iyyar. Ba za mu bari a tauye hakkin mambobinmu ba.”
A rabar Litinin Kwankwaso ya isa Kano, kuma ana sa ran zai gana da abokan siyasarsa domin tattauna dabarun zabe da tarukan jam’iyya kafin zaben 2027.
Sai dai Mai Riga ya nuna cewa tsohon gwamnan bai yi mu’amala kai tsaye da kwamitin zartarwa na jiha ba, sai dai ya tura tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam, ya jagoranci tattaunawa.
A martaninsa, kakakin tafiyar Kwankwasiyya, Mansur Kurugu, ya ce Kwankwaso da magoya bayansa ba su shiga Jam’iyyar NDC domin karbe iko ba, sai dai domin bunkasa jam’iyyar.
Ya ce, “Babu wata matsala a nan. Shugabancin kasa ne ya dakatar da taron, kuma za a gudanar da shi nan ba da jimawa ba. Babu wanda zai kwace komai daga wani.”
Kurugu ya kara da cewa, “Tabbas ba za ka sa mutum irin Kwankwaso ya shiga jam’iyya ba tare da ya samu tasiri a jiharsa ba. Amma ciyaman na jam’iyya ya kwantar da hankalinsa, za a gudanar da taron, kuma kowa zai samu abinda ya cancanta.”