Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi

Na yi kewar wannan fili na Camp Nou ƙwarai. Ina fata wata rana zan dawo in sake taka leda.

Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi

Lionel Messi

Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa.

Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan dawo in sake taka leda a nan gaban masoyana kafin in yi ritaya.”

A shekarar 2021 Messi ya bar Barcelona bayan matsalolin kuɗi da suka dabaibaye kulob ɗin, inda ya koma Paris Saint-Germain (PSG) ta Faransa, kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa Inter Miami ta Amurka bayan shekaru biyu.

Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau takwas, ya ƙara da cewa ziyarar da ya kai Camp Nou ta sake jaddada masa irin farin cikin da yake ji a duk lokacin da yake wannan fili.

“Camp Nou wuri ne da yake sa ni farin ciki matuƙa. Ina fatan zan dawo ba wai kawai don yin bankwana ba, har ma don sake taka leda a matsayin ɗan wasa.”

An gano baƙin haure 30 a ɓoye cikin tankar mai a Turkiyya

An tsare ɗan gwagwarmaya kan sukar gwamnatin sojin Nijar

Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida

Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida