Iran ta sake rufe Mashigar Hormuz, ta zargi Amurka

Masana na ganin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba a lamarin.

Iran ta sake rufe Mashigar Hormuz, ta zargi Amurka

Tashin hankali ya ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan da Iran ta sanar da sake rufe Mashigar Tekun Hormuz.

Iran ta zargi Amurka da saba yarjejeniyoyin da aka cimma a baya, da kuma ci gaba da hana jiragen ruwan Iran kai wa ga tashoshinta.
’Yan ta’adda sun kashe mutum 3, sun jikkata 6 a ƙauyen Sakkwato

Ta bayyana dalilin cewa ta yi hakan ne saboda matakan takunkumi da Amurka ke ci gaba da sanya wa jiragen ruwan ƙasar.

Mashigar tekun Hormuz hanya ce mai matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin duniya, domin kuwa ana jigilar kaso mai yawa na man fetur ɗin duniya ta wannan hanya a kowace rana.

Rufe hanyar na iya yin sanadiyyar tashin farashin mai a kasuwannin duniya baki ɗaya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya jaddada cewa ƙasarsa ba za ta ja da baya ba.

Ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da toshe mashigar har sai an kammala wata sabuwar “yarjejeniya” da Iran, kodayake bai yi ƙarin bayani kan abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa ba.

Sai dai kuma, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa har yanzu mashigar a buɗe take ga jiragen kasuwanci.

Ya ƙara da cewa ana gudanar da zirga-zirgar jiragen cikin tsari, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a ƙasar Lebanon.

Wadannan kalamai masu karo da juna sun haifar da ruɗani ga kamfanonin jigilar kaya da kuma masu lura da al’amuran duniya, waɗanda ke ƙoƙarin tantance sahihancin halin da ake ciki da kuma matakin tsaron wannan hanya.

A gefe guda kuma, Shugaba Trump ya bayyana cewa an dakatar da Isra’ila daga ci gaba da kai hare-hare a Lebanon.

An fara wanzar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 10, matakin da ya bai wa dubban mutanen da suka tsere daga gidajensu damar komawa muhallansu.

Masana na ganin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba a lamarin.

Sun yi gargaɗin cewa duk wani kuskure da aka samu a yankin Tekun Fars, zai iya janyo babban rikicin da zai shafi yankin baki ɗaya.

A kwanaki masu zuwa ake sa ran ganin ko tattaunawar diflomasiyya za ta samar da maslaha, ko kuma rikicin zai ƙara tsananta.