Sibil Difens ta lalata gidan sayar da jarirai, ta ceto mutum 28 a Legas

Jami’an hukumar sun samu nasarar latata gidan, bayan samun bayanan sirri.

Sibil Difens ta lalata gidan sayar da jarirai, ta ceto mutum 28 a Legas

Jami’an Hukumar tsaro ta Sibil Defens (NSCDC) reshen Jihar Legas, sun gano tare da lalata wani gida da ake zargin matattarar sayar da jarirai ne a yankin Badagry, inda suka ceto mutum 28 tare da kama wasu mutane biyu.

Kwamandan hukumar na jihar, Adedotun Keshinro ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Juma’a a Badagry, yana mai cewa an gudanar da samamen ne bayan shafe mako uku ana tattara bayanan sirri.

Keshinro ya ce, haramtacciyar matattarar da suke gidan, wacce take a Okuju, Ilado, Titin 1, Shiyya ta 1, Olorunda, an kai mata samame ne a wani bincike da aka yi cikin dare tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Afrilu.

Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun yi amfani da shafin Facebook wajen daukar mata masu juna biyu tare da lallashinsu su sayar da jariran da suka haifa ga masu bukata a kan kudi tsakanin ₦500,000 zuwa Naira miliyan daya.

An ceto mutane 28 daga gidan, ciki har da mata 17 masu juna biyu, babban namiji guda daya, da yara 10 wadanda wasu daga cikinsu jarirai ne, inda har aka ba da rahoton cewa mace guda ta rasa juna biyun nata saboda mummunan yanayin wurin.

Abubuwan da aka ƙwato sun hada da: injin famfo, janareta, fankoki guda shida, silindar iskar gas guda biyu da risho, manyan tukunyar girki, wayoyin salula ƙirar Android guda biyar, manyan tabarmi guda huɗu, da kuma kayayyakin abinci iri-iri.

Kwamandan ya yi Allah-wadai da wannan dabi’a a matsayin rashin imani, yana mai gargadin masu aikata laifi su daina ko kuma su fuskanci fushin doka.